Babu sojojin ƙasar waje a yankinmu —Sakkwatawa
Al’ummomin Sakkwato sun ce babu sojojin ƙasar waje a yankunansu kuma babu wani daji ko kauye mai sunan da shugaban ƙasar Nijar ya yi zargin an kafa sansanin sojojin ƙasar waje
Al’ummomin yankunan da ke kan iyakar Najeriya da Nijar sun musanta samuwar Dajin Gaba da Shugaban ƙasa Nijar, Abdurrahman Tchani, ya yi zargin ana kafa sansanin sojojin kasar wajen.
Mazauna da sarakunan yankunan Jihar Sakkwato da ke iyaka da Nijar sun shaida wa wakilinmu cewa babu wani daji mai wannan suna da Janar Tchiani ya ambata.
Wakikinmu ya ziyarci yankin inda a iya binciken da ya gudanar, babu Dajin Gaba.
Shugabannin yankin sun kuma musanta cewa akwai wasu sojojin ƙasashen waje da suka kafa sansani a yankunan nasu.
- Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024
- Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya
Jihar Sakkwato da ke Najeriya ta yi iyaka da Jamhuriyar Nijar ta ƙananan hukumomi biyar da suka hada da Illela, Gada, Tangaza, Gudu da kuma Sabon Birni.
Hasali ma, wasu daga cikin yankunan Nijar na daga cikin tsohuwar Daular Sakkwato.
A Ƙaramar Hukumar Illella Sarkin Arewan Araba, yankin da ke da nisan kilomita biyu daga yankin Konni, Alhaji Abubakar Yusufu, ya shaida wa wakilinmu cewa babu wani ƙauye ko daji mai suna Gaba a yankin.
Basaraken ya kuma yi watsi da ikirarin shugaban kasar Nijar cewa an kafa sansanin sojojin ƙasar waje a yankin illela.
Basaraken ya nuna fargaba cewa zargin da Janar Tchiani ya yi ma iya ƙara tsamin dangantaka tsakaninsu da makwabtansu na Nijar.
“Babu wani daji mai wannan suna a yankin Masarautar Araba ko ƙaramar hukumar Illela kuma babu wasu sojojin ƙasashen waje da muka gabi, saboda haka wanna maganar teburin mai shayi ne.
“Maimamakon haka ma sojojin Nijar ne ke zuwa garuruwan namu kowane dare.
“Suna zuwa su yi aiki tare da ’yan banganmu domin samar da tsaro a cikin al’ummominmu,” in ji shi.
Basaraken ya ja hankalin shugaban na Nijar da cewa yin zargi mata tushe na iya dagula daɗaɗɗiyar dangantaka da hulɗar diflomasiyya tsakanin ƙasashen masu maƙwabtaka da juna ta fuskan al’ada da ’yan uwantaka.
Wani mazaunin garin na Araba, Malam Muhammadu Danladi ya yi watsi da zargin da cewa shugaban Nijar ya yi ne domin bata sunan Najeriya.
“Ƙarya ce, babu sojojin ƙasashen waje a yankinmu, zargin ba shi da tushe,” in ji shi.
Ya kuma koka bisa abin da ya kira cin zalin da sojojin Nijar kem1q al’ummomin yankin a watanni shida da suka gabata.
Ya ce, “Jimi’an tsaronsu sai cin zalinmu suke ci, suna ƙwace mana kaya haka kawai. Amma su mutanensu babu mai takura su, su shiga su fita daga Najeriya babu mai ce musu komai. Ya kamata gwamnati ta ɗauki mataki.”