Babu son zuciya a rumfunan zaben da aka kara – Jega

Shugaban Hukumar Zabe ta kasa Farfesa Attahiru Jega ya ce babu son zuciya a rumfunan zabe dubu 30 da aka kara a kasar nan. Kuma ya ce kara rumfunan zaben bai saba ka’ida ba, an kuma bi dukkan matakan da suka dace kafin hukumar zabe ta kara yawan rumfunan a kasar nan.Farfesa Jega ya bayyana […]

Babu son zuciya a rumfunan zaben da aka kara – Jega
Babu son zuciya a rumfunan zaben da aka kara – Jega

Shugaban Hukumar Zabe ta kasa Farfesa Attahiru Jega ya ce babu son zuciya a rumfunan zabe dubu 30 da aka kara a kasar nan. Kuma ya ce kara rumfunan zaben bai saba ka’ida ba, an kuma bi dukkan matakan da suka dace kafin hukumar zabe ta kara yawan rumfunan a kasar nan.
Farfesa Jega ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja a shekaranjiya Laraba, inda ya ce babu zancen siyasa ko bangaranci dangane da karin, don haka hukumar zabe ba za ta janye batun kara rumfunan zaben ba.
A kwanakin baya ne hukumar ta sanar da kara rumfunan zabe dubu 30, inda suka koma dubu 150, sai dai karin ya haifar da cece-kuce, inda wasu suka rika cewa akwai siyasa a ciki, wasu kuma suka ce an fifita wani bangare a kara rumfunan da aka yi.
Shugaban ya ce hukumarsa ta yi adalci wajen kara rumfunan zaben a jihohin Najeriya 36 da Abuja.
Ya ce ya ji cece-kucen da ake ta yi a kan kara rumfunan zaben duk cewa hukumarsa ba ta fito da yadda ta rarraba rumfuna dubu 30 da aka kara ba.
“Hukumar INEC ta yanke shawarar sake fasalin rumfunan zabe da kara wasu, don haka ina so mutane su fahimci an yi haka ne don inganta zabe a kasar nan, kuma babu wata boyayyiyar manufa, ko batun bangaranci dangane da batun,” inji shi.
Farfesa Jega ya ce yawan Najeriya ya karu da kashi 60 cikin 100 bayan kirkiro rumfunan zabe dubu 120 a 1996, don haka ya zama tilas a kara wasu don a samu damar gudanar da ingantaccen zabe.
Akwai jihohi 17 da suke da kashi 30 cikin 100 na rumfunan zabensu da suke da mutane 750 a kowace rumfar zabe, sannan akwai jihohin da fiye kashi 50 ko 60 cikin 100 na rumfunan zabensu suke da irin wannan matsalar ta fiye da mutum 500 a kowace rumfa.
“A Birnin Tarayya babu rumfunan zabe a APO Gwari da Asokoro New Edtension da rukunin gidajen FCDA kuarters Area 3 da rukunin gidajen ma’aikatan Babban Bankin Najeriya, da ke hanyar garin Garki da Games billage,” inji shi.
Ya ce don haka akwai bukatar kara rumfunan zabe, amma wasu jihohi suna da rumfunan zaben da suka fi yawan masu zabe, amma duk da haka hukumar ta amince ta kara rumfunan zabe akalla 121 a kowace jiha da kuma Abuja.
Ya nuna wa ’yan jarida teburin yawan rumfunan zabe a Najeriya, inda Jihar Anambra da Bayelsa da Ekiti da Enugu da Osun ke da rumfunan zaben da suka yi musu yawa, amma duk da haka an kara musu kashi 15 cikin 100 na rumfunan zaben.
Ya ce hukumarsu ba ta yi la’akari da yawan mutanen kowace jiha wajen karA rumfunan zaben ba, sai dai ta yi amfani da yawan jama’ar da suka yi rajistar katin zabe, inda yawan wadanda suka yi rajistar ya kai miliyan 70 da dubu 383 da 427 a kasa baki daya.
“Hanya mafi sauki ta raba rumfunan zabe dubu 150 ita ce, a raba yawan wadanda suka yi rijista zuwa mutum 500 a kowace rumfa. Don haka INEC ba ta da niyyar janye karin rumfunan zabe duk da korafin da ake yi, saboda abin da ta yi bai saba wa doka ba,” inji shi.