Babu soyayya tsakanina da Hamisu Breaker – Momee Gombe

Ta ce aiki ne kawai yake hada su, ba soyayya ba

Babu soyayya tsakanina da Hamisu Breaker – Momee Gombe

Fitacciyar jarumar Kannywood Maimunatu Abubakar wacce aka fi sani da Momee Gombe, ta ce abin da ke tsakaninsu da da matashin mawakin nan Hamisu Breaker ba soyaya ba ce, ba kamar yadda mutane suke dauka.

Jarumar ta bayyana haka ne a hirarta da Hadiza Gabon a cikin shirinta na hira da taurarin masana’antar mai suna ‘Gabon’s Room Talk Show’ a dandalin sada zumunta na ‘YouTube’.

Jarumar ta ce mutane ne kawai suke irin wannan tunani saboda ganin suna huldar aiki a masana’antar.

Sai ta kara da cewa mawakin abokin sana’arta ne kawai.

“Da zarar mutane sun ga kana hulda da mutum sai su ɗauka soyayya ce, amma maganar gaskiya ban taɓa soyayya da shi ba. Babu soyayya da ke tsakanina da shi illa iyaka abokin sana’a ne kuma muna da kyakkyawar fahimta a tsakaninmu shi ke nan,” in ji jarumar.

Dangane da yadda ta shigo Masana’antar Kannywood, jarumar wacce tauraronta ke haskawa ta ce, Furodusa Usman Mu’azu wanda shi ma ɗan asalin Gombe ne ya yi silar shigowarta harkar fim.

“Usman ya kasance kamar  ɗan gida ne a gidanmu, babu inda ba ya shiga a gidanmu, ni kuma ina yawan tambayarsa cewa ina so in shiga harkar a duk lokacin da suka zo ɗaukar fim a Gombe. Sai shi kuma ya ce ba za a
bar ni a gida ba, amma daga bisani da na matsa sai aka bar ni na fara harkar
fim ɗin,” in ji ta.

Shirin na Hadiza Gabon ya yi farin jini inda take hira da jarumai da mawaka a salon tambayar kwakwaf da a wasu lokuta sukan janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a, musamman wadanda suke kallon abin da take yi a matsayin kutse da kuma nuna rashin sani makamar aikin jarida.