Babu sulhu sai Kwankwaso ya rubuta takardar neman gafara – Kwamsihina

Gwamnatin Jihar Kano ta gindaya sharadin cewa kafin a yi maganar sulhu a tsakanin  bangaren Gwamnan Jihar da ake kira Gandujiyya da bangaren tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ake kira Kwankwasiyya, sai Sanata Rabi’u Musa Kwankwao ya rubuta takardar neman yafiya zuwa ga Gwamna Abdulllahi Umar Ganduje kan kalaman batanci da shi […]

Babu sulhu sai Kwankwaso ya rubuta takardar neman gafara – Kwamsihina

Gwamnatin Jihar Kano ta gindaya sharadin cewa kafin a yi maganar sulhu a tsakanin  bangaren Gwamnan Jihar da ake kira Gandujiyya da bangaren tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ake kira Kwankwasiyya, sai Sanata Rabi’u Musa Kwankwao ya rubuta takardar neman yafiya zuwa ga Gwamna Abdulllahi Umar Ganduje kan kalaman batanci da shi da  magoya bayansa suka rika yi ga Gwamnan da gwamnatinsa.

Kwamishinan Watsa Labarai, Matasa da Wasanni, Kwamared Muhammad Garba ne, ya bayyana haka a lokacin da yake tatatunawa da manema labarai a Kano.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kwamitin da ke kokarin sulhunta ’ya’yan Jam’iyyar APC a karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Jihar Legas Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ke kai ziyara ga jihohin da ke da matsala a tsakanin ’ya’yan jam’iyyar inda ake sa ran ya ziyarci Jihar Kano da nufin dinke barakar da ke tsakaninsu.

Sai dai masu fashin bakin siyasa na ganin sulhun zai yi wuya a Kano sakamkaon sharuddan da bangaren Gandujiyya ya gindaya cewa dole sai bangaren Kwankwasiyya sun cika su matukar ana bukatar yin sulhu a tsakaninsu.

Kwamishinan Watsa Labaran na Jihar Kano ya ce babban matakin sulhu shi ne ’yan Kwankwansiyya wadanda suka yi ta batanci ga gwamnatin Ganduje su fito su nuna nadamarsu a kan abin da suka yi. “Ya kamata wadanda suka yi ta batanci ga wannan gwamnati da kuma Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje tun daga kan jagoransu Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da Kwamared Aminu Abdussalam da Dokta Yunusa dangwani da Janar Bello Dambazau su rubuto takardar neman afuwa ga Mai girma Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje bisa kalaman batanci da suka rika yi masa,” inji shi.

Kwamishinan ya ce idan har ’ya’yan bangaren Kwanwasiyyar suka cika wancan sharadi to Gwamna a matsayinsa na Khadimul Islam zai hakura ya karbi sulhun. “Na tabbata idan suka yi haka Mai girma Gwamna a matsayinsa na Khadimul Islam zai duba abin da takardar ta kunsa kuma na tabbatar zai yafe musu,” inji shi.

Kwamishinan ya kara da cewa “Ita wannan takardar ita ce za ta nuna cewa sulhun da masalahar da za a yi  da gaske za a yi su. Ba ma son sai an yi sulhu a zo a yi mana burum-burum. A ce an shirya a karshe a zo ana yi mana zagon kasa. Ka ga idan aka yi haka bai zama an yi sulhu na gaskiya ba. Muna so idan an yi sulhu ya zama an yi shi bisa amana da gaskiya ta yadda kowa zai zo ya bayar da gudunmawa domin nasarar jam’iyya da kuma gwamnati tare da ci gaban al’ummar Jihar Kano gaba daya.”

A kwanakin baya dai an jiyo Gwamna Ganduje yana barranta kansa da Kwankwasiyya tare da shan alwashin ba zai taba yin sulhu da Kwankwasiyya ba. “Wai ’yan Kwankwasiyya suna so a daidaita, wacce irin daidaitawa? To idan aka daidaita yaya za mu yi da sanya jar hula, sai mu dawo mu ce kowa sai ya sa jar hula ke nan? Mu da Kwankwasiyya haihata-haihata, idan ba ka san Hausa ba ka je a fassara maka kalmar haihata-haihata,” inji Gwamnan.

Da Aminiya ta tuntubi daya daga cikin wadanda Kwamishinan ya ce sai sun rubuta takardar neman afuwa ga Gwamna Ganduje, wato Dokta Adamu Yunusa dangwani wanda kusa ne a tafiyar Kwankwasiyya ya ce ba za su taba rubuta takardar neman afuwa ba, kasancewar su aka yi wa laifi don haka su ya kamata a nemi afuwarsu. “Ban taba ganin inda aka yi haka ba, yaya za a yi wanda aka yi wa laifi a ce kuma shi zai nemi afuwar wanda ya yi masa laifi? Shugabanka wanda Allah ne Ya dora ka, shi ne Ya dora ka, amma ka zo kana yin wasu surutai a kansa har kana cewa sai ya zo ya nemi afuwarka? Mutanen Kano masu hankali ne haka kuma jama’ar Najeriya duk sun san abin da ya faru don haka sun isa su yi hukunci,” inji shi.

A cewar Dokta dangwani shure-shure ne bangaren Gandujiyya yake yi wanda kuma ba ya hana mutuwa, “Sun hango tafiyar ba za ta yi musu kyau ba ne, don haka suke ta biye-biyen sulhu. Kame-kame suke yi domin a samu sulhu a tsakaninmu. Kin san duk mutumin da ba ya da daraja to dole ya yi kokarin rabar mutumin da ke da daraja don shi ma ya same ta,” inji dangwani.

Har ila yau dangwani ya musanta batun da bangaren Gandujiya ke yi cewa Gwamna Ganduje ya nemi sulhu da tsohon Gwamnan Kwankwaso har sau 17 amma abin bai yi nasara ba. “Wannan magana da Gwamna ya yi ba gaskiya ba ce ba a yi ta ba, domin mu a iya saninmu babu wani lokaci da aka yi hakan ko sau daya ba a yi hakan ba,” inji shi.

Dokta dangwani ya bayyana Kwamishinan Watsa Labaran a matsayin dan shan romon siyasa a sama, a cewarsa lokacin ma da aka kafa gwamnatin ba ya nan, “Ina mamakin yadda shi mai maganar yake da karfin halin yin wadannan surutai, mutumin ma da lokacin da aka yi wa jam’iyya wahala da kuma kafa gwamnatin ta Ganduje ba ya nan. Bai san wahalar komai ba, ya zo daga yana cin gwamnati a sama, har irin wannan mutumin yana da bakin magana? Bai cancanta ma ya zo yana wasu surutai ballantana ya gaya mana yadda za a yi sulhu. Sai dai shi uban gidansa ya fito ya gaya mana da bakinsa,” inji shi.  

Da Aminiya ta tambaye shi ko za su amince da sulhun da Kwamitin Bola Tinubu zai yi musu, sai ya ce “Su wane ne a Kwamitin Tinubu? Shi kadai ne fa. To mu a shirye muke Tinubu ya zo, mun san abin da za mu gaya masa muna da hujjojinmu a kan haka. Mun ce sulhu tsakaninmu da Gandujiyya har abada!”