Babu talakan da zai sake zaben APC a Najeriya – Kawule
Honarabul danlami Ahmed Kawule tsohon dan Majalisar Jihar Bauchi ne wanda ya wakilci mazabar Zungur/Galambi/Miri a lokacin mulkin Gwamna Isa Yuguda yanzu kuma shi ne Shugaban kungiyar Fardado da Jam’iyyar PDP na kasa. A tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana dalilin da ya sa suka kafa kungiyar kuma ya ce babu talakan da zai sake zaben […]
Honarabul danlami Ahmed Kawule tsohon dan Majalisar Jihar Bauchi ne wanda ya wakilci mazabar Zungur/Galambi/Miri a lokacin mulkin Gwamna Isa Yuguda yanzu kuma shi ne Shugaban kungiyar Fardado da Jam’iyyar PDP na kasa. A tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana dalilin da ya sa suka kafa kungiyar kuma ya ce babu talakan da zai sake zaben Jam’iyyar APC:
Aminiya: Me ya sa kuka kafa kungiyar farfado da PDP?
Kamar yadda aka sani ni Honarabul danlami Ahmed Kawule Baraden Galambi, ni ne sabon shugaban kungiyar farfado da PDP wato PDP Riberanding Forum na kasa. Mun kafa kungiyar ce domin ci gaba da yayata manufofin jam’iyyarmu ta PDP. Mun shekara 16 muna mulki a Najeriya kowa ya ga kamun ludayinmu mun yi wasu kura-kurai irin na dan Adam. Kuma kafin zaben shekara ta 2019 muna fatar za mu gyara kura-kuranmu tunda yanzu talakawa sun ga bambancin da ke tsakanin PDP da APC. Ya rage wa talakawa su zabi jam’iyyar da za ta bunkasa rayuwarsu tare da rage radadin talauci a tsakanin al’umma.
Yaushe aka kafa wannan kungiya da kake shugabanta?
An kafa wannan kungiya ce wata shida da suka gabata, kuma jihohi da dama suna da shugabannin wannan kungiya. Manufarmu ita ce bayyana wa al’umma dalilan da suka sa muka fadi a zaben 2015 kuma wasu hanyoyi za mu bi domin sake kafa gwamnati a shekarar 2019. Shugabanci wani abu ne mai matukar wahala ba kowa ke fahimtar haka ba, duk abin da za ka yi wadansu ba sa gani, babu abin da ba a fada wa ’yan PDP a lokacin zaben bara, wadansu ma har kafirta mutane sun yi. Yanzu an gudanar da taro inda aka amince da tsarin shugabanci na karba-karba na wadanda za su nemi kujerar shugabancin PDP na kasa. Mutane da dama daga kudancin kasar nan sun fito takara amma abin da muke so shi ne a zabi shugabannin masu jini a jika. Domin duk Afirka babu jam’iyyar da ta kai PDP girma da dimbin magoya baya a birni da karkara, ba kowa zai fahimci haka ba sai a shekarar 2019 inda za mu karbe mulki daga hannun APC. Wannan kungiya za ta yaki duk wani mutum wanda ya fito takarar shugabancin PDP wanda bai cancanta ba domin ba ma so a sake fasawa kowa ya rasa, kowa ya ga abin da ya faru a shekarar 2015. dauki-dora ya kare a Jam’iyyar PDP tun daga matakin unguwannin har zuwa kasa sai wanda ya cancanta za mu goya masa baya. Kuma rashin ba da dama ga matasa a PDP na daya daga cikin abubuwan da suka kawo mana koma baya a kasar nan, sannan ba da tikitin takara ga tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan na daga cikin abubuwan da suka sa PDP ta fadi a bara.
Kana ganin har yanzu talakawa na kaunar PDP?
Ina tabbatar maka da cewa har gobe akwai dimbin talakawan da suke kaunar PDP a zuciyarsu domin lokacin mulkinmu mutane da dama sun samu aikin yi, wadansu sun mallaki motoci da gidaje wadansu kuma sun samu jari mai tsoka saboda haka muna da magoya baya fiye da kowace jam’iyya a Najeriya. Yau in aka shirya zaben-gwaji tsakanin APC da PDP ina tabbatar maka cewa kadan ne za su zabi APC a Najeriya, domin babu wani aiki da za su nuna wa talakawa a kasa wanda suka kammala tun daga hawansu mulki. Lokacin da PDP ke mulki shinkafa da sauran kayan abinci ba su yi tsada ba domin gwamnati tana shimfada ayyukan alheri wadanda aka zaba suna kyautata wa mutanen mazabarsu daidai gwargwado sabanin yanzu. Zaben shekara ta 2019 jihohin da PDP za ta kafa gwamnati za su yi yawa domin yanzu kowa yana ji a jikinsa, talauci da tsadar rayuwa sun shafi kowa kudi kuma ya yi karanci a hannun al’umma sakamakon yadda gwamnatocin suka gagara ba da kwangila da sauran nade-nade na siyasa.
Me za ka ce kan gwamnatin Jihar Bauchi?
Gwamnatin Jihar Bauchi tana dauke da dimbin matsaloli, albashin ma’aikata ya gagara ga ’yan fansho na cikin mawuyacin hali sama da kasha 50 na mutanen Bauchi suna ga kamar ba mulki ake yi ba.
Mene ne sakonka ga shugaban kasa Muhammadu Buhari?
Babban abin da zan fada wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayina na dan PDP shi ne ya kamata ya fahimci talakawa ba sa iya cin abinci sau uku a rana ’yan kasuwa da dama sun rufe shagunansu da sauran dimbin matsaloli. Bayan haka wajibi ne Shugaban kasa ya taka birki ga gwamnoninsa na APC da ke ganin sun fi fadar Shugaban kasa iko a tilasta musu biyan ma’aikata hakkokinsu.
Mene ne sakonka ga magoya bayan PDP?
Babban sakona ga daukacin magoya bayan PDP a kasar nan shi ne mu ci gaba da hakuri kuma kada mutum ya sauya sheka zuwa wata jam’iyya, kowa ya gyara zuciyarsa tsakani da Allah wannan shi ne abin da zan fada a takaice. Sakona ga ’yan siyasa shi ne a kama sana’a domin yanzu ba lokacin yawon tsegumi ba ne a tsakanin al’umma, APC ta ba da gudunmawa wajen rage masu yawon tsegumi a tsakanin ’yan siyasa kowa an ce ya kama sana’a. Sannan mu ci gaba da hakuri domin yanzu mun gagara fahimtar ina aka dosa. Allah Ya kara mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.