Babu wadanda gwamnati ta yi watsi da su a Najeriya kamar mutanen Jos – danladi Pasali
daya daga cikin fitattun mutane Jos kuma Sakataren Kudi na kungiyar Masu Gidajen Mai ta kasa, Alhaji danladi Garba Pasali ya ce a duk Najeriya mutanen Jos wadanda suka kai sama da miliyan daya kadai ne gwamnati ta yi watsi da su ba ta yin komai da su. Alhaji danladi Pasali ya bayyana haka ne […]

daya daga cikin fitattun mutane Jos kuma Sakataren Kudi na kungiyar Masu Gidajen Mai ta kasa, Alhaji danladi Garba Pasali ya ce a duk Najeriya mutanen Jos wadanda suka kai sama da miliyan daya kadai ne gwamnati ta yi watsi da su ba ta yin komai da su.
Alhaji danladi Pasali ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wurin taron kaddamar da gidauniyar da kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Filato ta shirya a Jos, don gudanar da wasu ayyukan Musulunci.
Ya ce “Duk da yawan jama’a da mu mutanen Jos muke da su, gwamnati ba ta yin komai da mu a unguwanninmu da karamar hukumarmu da Jihar Filato da tarayya, an mayar da mu kamar wadansu Falasdiwa, saboda wai mu baki ne.”
Ya ce don haka “A yau mu kadai ne muke da dimbin yara masu shaye-shaye da ba su da aikin yi, mu mutanen Jos muna neman gudunmawa a rika daukar ’ya’yanmu aiki a duk matakan gwamnati.”
Alhaji danladi Pasali ya ce ilImi shi ne rayuwa, don haka ya nuna farin ciki kan yadda kungiyar Izala ta sanya harkokin ilimi a kan gaba. “Duk lungun da aka duba a garin Jos za a ga makarantar kungiyar, wannan ne ya tallafa wa mutanen Jos wajen sanya ’ya’yansu a makarantu kuma wadannan makarantu sun samar da mutanen Jos masu digiri sama da dubu daya.
A jawabin shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar na kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga Musulmin Najeriya kan su kara hada kansu bisa gaskiya.
Sheikh Sani Yahya Jingir wanda Sa’in kungiyar na kasa Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya wakilita ya ce da da’a da mutunci da cika alkawari ake sanin mutumin kwarai, “don haka mu rungumi
wadannan abubuwa, mu yi kokari mu yi karshe mai kyau,” inji shi.
Shugaban majalisar malamai ta kungiyar ta Jihar Filato Dokta Hassan Abubakar Dikko ya ce an shirya taron ne, domin a tara gudunmawar da za su bayar a lokacin kaddamar da gidauniyar raya ilImi ta kasa da kungiya take yi a kowace shekara da kuma wasu ayyukansu na ilimantarwa a jihar.