Babu wanda ke tunawa da ni sai ‘yan Jarida – Hassan Wayam

Shahararren mawakin Kukumar nan, Hassan Wayam ya ce yana nan a raye lafiya. Ya bayyana haka ne a tattauwarsa da Aminiya a gidansa da ke Layin Zomo, Falladan karamar Hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna. Ana ta rade-radin cewa ka rasu? Alhamdullahi! har yanzu ina nan a raye da sana’ata, kuma har yanzu a na […]

Babu wanda ke tunawa da ni sai ‘yan Jarida – Hassan Wayam

Shahararren mawakin Kukumar nan, Hassan Wayam ya ce yana nan a raye lafiya. Ya bayyana haka ne a tattauwarsa da Aminiya a gidansa da ke Layin Zomo, Falladan karamar Hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna.


Ana ta rade-radin cewa ka rasu?

Alhamdullahi! har yanzu ina nan a raye da sana’ata, kuma har yanzu a na nan ana tabawa amma ba kamar da ba. Da ka san ina da kulob da nake wasa a Zariya wato Kulob din Lebanon ina yi wasa a ranakun Asabar da Juma’a. Kuma duk wanda zai shiga sai ya biya, kuma nan ne nake samun abin masarufi. To wani tashin hakalin da ya faru a lokacin zabe wanda hatta masallaci sai da aka hana zuwa, to sai na yanke shawarar in hakura da fita tun daga sannan ban sake fita wasa a kulob ba sai dai idan an nemi ni a gidan biki, ko  wajen taro, ko a ina ne zan iya zuwa in yi amma in ba haka ba kullum ina gida.

Ko za ka bayyana mana takaitaccen tarihinka?

To gaskiya sai dai kwatance, an ce a lokacin da aka kashe Sardauna ina da shekara kusan 15 don ka san mutanen kauye ba za a iya ganewa ba, to amma zuwana garin Zariya sojoji suka kawo ni a 1969, kuma tun lokacin na fara waka kamar shekara uku, bayan kashe Sardauna, kuma dama sabo da fasahar waka ce wani soja ya dauko ni zuwa Zariya. Batun yawan wakokina kuwa ba zan iya sani ba domin inda duk ka bincika ita waka baiwa ce daga Allah, kuma duk mawaki in dai mawaki ne da Allah Ya yi wa fasaha, to bai iya cewa ga iyakar wakarsa. Maganar wakar da na fi so kuwa akwai wakar da ake cewa a noma gero a noma dawa kuma a noma alkama ’yar bakin ruwa, wato wakar manoma, ita na fi so, sai wakar da ake ce wa talala walkin maciji kamar ya katse ba zai katse ba soyayya ruwan zuma ce kowa ya sha ya ba masoyi.

Ka taba samun lambar yabo a harkar waka?

Ban taba samun lambar yabo ba domin ni ban taba zuwa ko’ina da waka ba in ban da nan kasar.

Mece ce gaskiyar maganar an taba kama ka a kasar Nijar?

Ni ma haka nake ji, amma ban taba zuwa kasar Nijar ba, kai ba ma kasar Nijar ba ni Hassan Wayam tunda Allah Ya yi ni ban taba zuwa kasar waje ba sai aikin Hajji.

Wane bayani za ka yi a kan yadda harkar wakoki ke gudana yanzu?

Wato idan ka duba wakoki sun kasu kashi biyu: Akwai wakoki irin namu, akwai na yanzu kuma wato wakokin zamani, wakokin zamani ba su cika dadewa ba, domin ka ga ai baya an yi yayin ’yan gurmi sun taso baga-baga sai aka tsaya, kuma aka zo ana yayin asharalle baga-baga su ma suka tsaya, yanzu kuma masu wakar fim sun taso tun suna cewa fadakarwa suke yi, to yanzu su ma abin nasu ya zama sana’a kuma ka gani yanzu sun mayar da abin ba tsari domin da zarar sun ji cewar ana biki gidan wane to sai ka ji sun yi masa kaset sun kai masa, ko ko ba a sa su ba. Mu ko ka ga makadan da ba haka muke ba, sai an kira mu taro muke zuwa mu je fasaharmu, amma su akasarinsu da kaset suke zuwa. Ba wai mun raina fasaharsu ba ce. Yanzu kowa waka yake yi, wata wakar ma idan ka ji sai ka ji kamar kukar mage, ka ma kasa fahimtar me ake cewa a wakar. Kuma yanzu misali da ka zo gidana sai ka ce Hassan Wayam yi mini waka, nan take kawai zan yi har sai hankalinka ya tashi har ma ka yi mana alheri.

Yanzu matanka da ’ya’yanka nawa, kuma kana da magaji a ’ya’yanka?

Ina da mace daya yanzu da ’ya’ya hudu sai jikokina, dana da ya rasu ya bari su biyar, kuma a yanzu ba ni da magaji domin wanda na sa rai zai gaje ni lokacin da aka yi rikicin zabe sojoji sun harbe shi, don haka a yanzu ba ni da mai gadona.

Ko kana da wani abu da kake so ka fadi ga jama’a?

Akwai domin halin da nake ciki ya zama halin lahaula wala kuwwata, idan ba ku ’yan jarida ba, babu wanda suke tuna wa da mu, kuma haka ma masu amfani da wakokinmu su ma ba sa tunawa da mu, haka masu sayar da wakokinmu sun manta da mu. Kuma tunda sojoji suka harbe min da a zamanin  mulkin Shugaba Goodluck Jonathan, ya rasu ya bar ’ya’ya biyar, babu wata gwamnati da ta yi min jaje, ko ta tausaya min har zuwa yau, kuma yanzu haka abin da za mu ci ma a gidan kusan gagara yake don wata rana garin rogo muke jikawa mu sha. Don haka ina kira ga ku ’yan jarida da gidajen rediyo da kuke damuwa da mu, ku ci gaba da taimaka mana musamman mu tsofaffin mawaka da tsofaffin masu fasaha da al’adu.