Babu wanda rikicin Kudancin Kaduna bai taba ba – Janar Agwai

Biyo bayan tashin-tashinar da aka rika fuskanta a Kudancin Kaduna, masu ruwa da tsaki a yanzu haka na tattaunawa a garin Kafanchan da ke karkashin karamar hukumar Jema’a ta jihar domin gudanar da yarjejeniyar sulhu da za ta kawo mafita mai dorewa game da rikicin da ya dabaibaye yankin. Da yake jawabi a wajen taron, […]

Babu wanda rikicin Kudancin Kaduna bai taba ba – Janar Agwai

Biyo bayan tashin-tashinar da aka rika fuskanta a Kudancin Kaduna, masu ruwa da tsaki a yanzu haka na tattaunawa a garin Kafanchan da ke karkashin karamar hukumar Jema’a ta jihar domin gudanar da yarjejeniyar sulhu da za ta kawo mafita mai dorewa game da rikicin da ya dabaibaye yankin.

Da yake jawabi a wajen taron, tsohon Hafsan Hafsoshin tsaro na Najeriya, Janar Martin Luther Agwai (mai ritaya) ya ce kashe-kashen da ake yi a Kudancin Kaduna ya shafi kowa ta yadda ba ya la’akari da bambancin kabila ko addini.

A dalilin haka ne tsohon sojan ya ke kira tare da bukatar duk masu ruwa da tsaki da su bi hanyar lumana da zai ta kai ga gaci na sulhu “a wannan zamana da duk mutane suka juya baya ga zaman lafiya.”

Janar Agwai wanda shi ne uban taro a zaman sulhun na kwanaki uku mai taken: “Dakile rikici a Kudancin Kaduna,” ya yi kira ga Gwamna Nasir El-Rufai da ya tashi tsaye wurjanjan kan rikicin Kudancin Kaduna domin tarihi ya tuna da shi a matsayin gwamna daya tilo da ya yi nasarar kawo zaman lafiya na dindindin a yankin.

Yayin wata hira da ya yi a baya bayan nan da manema labarai na jaridar BBC, Gwamna El-Rufa’i ya ce rikicin Kudancin Kaduna ya samo asali ne tun a shekarar 1980, lokacin da wasu suka far wa mutane a Kasuwar Magani tare da hallaka mutum 11.

Gwamnan yayin hikaito tarihi, ya ce rikicin ya kara rincabewa a 1992, inda wannan lokaci aka kashe kimanin mutum 1,300 a Zangon Kataf kan wata husuma game kasuwa.

Mahara sun kashe mutum 9 sun jikkata wasu a Nasarawa

Aikin titin tiriliyan 16 ya yi layar zana a kasafin 2025

An yi garkuwa da ’yar ƙasar waje a Nijar

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara