Babu wanda ya fi Sule Lamido cancantar shugabancin Najeriya -Nafi’u Jos
Shugaban kungiyar matasa magoya bayan tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya tsaya takarar shugabancin kasar nan, a shekarar 2019 karkashin PDP (NLYMGG) na shiyar jihohin Arewa ta Tsakiya, Nafi’u Ya’u Jos, ya bayyana cewa babu wanda ya cancanci ya zama shugaban Najeriya kamar Alhaji Sule Lamido. Nafi’u Jos ya bayyana haka ne a […]

Shugaban kungiyar matasa magoya bayan tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya tsaya takarar shugabancin kasar nan, a shekarar 2019 karkashin PDP (NLYMGG) na shiyar jihohin Arewa ta Tsakiya, Nafi’u Ya’u Jos, ya bayyana cewa babu wanda ya cancanci ya zama shugaban Najeriya kamar Alhaji Sule Lamido. Nafi’u Jos ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taro da wata kungiyar matasa masu fafutukar ganin Lamido ya tsaya takarar shugabancin kasar nan, a zaben 2019 reshen Jihar Filato a Jos.
Ya ce a duk gwamnonin da suka yi mulki a Jihar Jigawa, babu wanda ya yi aiki kamar Sule Lamido. Ya ce Sule Lamido ya yi ayyukan raya kasa da dama a Jihar Jigawa da suka hada da hanyoyin mota da samar da wutar lantaki da asibitoci da makarantu da ruwan sha.
“Alhaji Sule Lamido mutum ne mai hangen nesa, wanda babu ruwansa da maganar nuna bambancin addini ko na kabilanci. Don haka idan al’ummar Najeriya suka zabe shi, zasu ci gajiyar mulkin dimakoradiyya”.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar matasan masu fafutukar tsayawar takarar shugabancin kasar na Sule Lamido, (SLYMN) reshen Jihar Filato, Abdulhadi Abdullahi Cokali ya bayyana cewa wannan kungiya ce mai zaman kanta, wadda aka kafa ta watanni 10 da suka gabata. Ya ce wannan kungiya, wadda ta kunshi dukkan kabilun Jihar Filato, tuni ta kafa rassanta a dukkan mazabun jihar.
“Babban dalilin da yasa muka zabi mu goyawa Sule Lamido baya wajen ganin ya tsaya takarar shugabancin kasar nan, shi ne mun gano cewa babu wanda zai tafi da matasa idan ya zama shugaban kasar nan, kamar Sule Lamido”.