Babu wanda ya isa ya raba Najeriya – Jonathan
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya ce babu wanda ya isa ya raba kasar nan. Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga dubban magoya bayansa a garin Jos a lokacin da ya isa Jihar Filato a ci gaba da kamfe dinsa. Shugaba Jonathan ya ce Jihar Filato jiha ce da ta […]
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya ce babu wanda ya isa ya raba kasar nan. Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga dubban magoya bayansa a garin Jos a lokacin da ya isa Jihar Filato a ci gaba da kamfe dinsa.
Shugaba Jonathan ya ce Jihar Filato jiha ce da ta fitar da muhimman mutane irin su marigayi Cif Solomon Lar da Janar Yakubu Gowon, wanda a lokacin da yake shugabancin kasar nan ya tsaya wajen ganin kasar nan ta ci gaba da zama a hade bayan yakin basasa. Don haka ya ce za su ci gaba da koyi da wannan shugaba wajen ganin kasar nan ta ci gaba da zama a hade.
Shugaba Jonathan ya ce gwamnatinsa ta samu nasarar bunkasa ilimi da noma a kasar nan, kuma ta magance cutar Ebola. Ya ce idan aka zabe su za su daukaka kasar nan zuwa gaba.
A jawabin Mataimakinsa NamadiSambo ya ce daga mako mai zuwa za a fara zirga-zarga ta jirgin kasa daga Jos zuwa Fatakwal da Jos zuwa Bauchi zuwa Gombe da Jos zuwa Kafanchan zuwa Kaduna zuwa Kano da kuma Jos zuwa Legas zuwa dukkan sassan Najeriya.
Kuma ya ce Shugaban kasa ya amince a ware Naira biliyan 220 don tallafa wa masu kananan masana’antu a kasar na da kuma Naira biliyan 27 don bunkasa noman rani.
A jawabin shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu ya ce Jihar Filato ita ce cibiyar PDP a Najeriya, domin a jihar aka fara zaben Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo a matsayin dan takarar jam’iyyar a wannan jamhuriyya. Don haka ya ce al’ummar Filato ba za su bar Jam’iyyar PDP ba. Ya ce dukkan wadanda suka bar PDP, sun bar ta ne saboda son zuciyarsu ba don ci gaban al’umma ba.