Babu wanda ya kamu da COVID-19 cikin masu Umara miliyan 5 —Saudiyya

Saudiyya ta tabbatar da cewa babu ko da mutum daya daga cikin sama da miliyan biyar din da suka bakunci kasar domin ibadar Umar da ya kamu da cutar COVID-19.

Babu wanda ya kamu da COVID-19 cikin masu Umara miliyan 5 —Saudiyya

Al’ummar Musulmi suna Dawafi a Ka’aba

Kasar Saudiyya ta tabbatar da cewa babu ko da mutum daya da ya kamu da cutar COVID-19 daga cikin sama da miliyan biyar da suka bakunce ta domin ibadar Umar.

Ministan Harkokin Aikin Hajji da Umrah na kasar, Dokta Mohammed Saleh Benten ne ya bayyana hakan a birnin Jidda yayin wata ganawa da gwamnan Makkah, Yarima Khaled Al-Faisal.

Ministan ya ce adadin mutum fiye da miliyan biyar din na daukacin mutanen da suka gabatar da ibadar da aka ci gaba da gabatarwa ne bayan annobar COVID-19 ta sa an dakatar a baya.

Saudiyya ta dakatar da Umrah cikin watan Maris, daga bisani kuma ta sake takaita adadin mutanen da za su halarci aikin Hajji zuwa 1,000 kacal a kokarin takaita yaduwar cutar.

Sai dai kasar ta sake bayar da sanarwar dawo wa ci gaba da aikin Umrah jim kadan da janye dokar kulle da aka sanya a kasar tare da gindaya ka’idojin da jami’an lafiya suka shimfida na kariya daga cutar.

A ranar 22, ga watan Satumbar 2020, kasar ta sake bayar da sanarwar komawa ci gaba da Umrar, sannu a hankali kuma aka kara adadin masu yi wadanda aka karkasa zuwa rukuni hudu.

A karon farko cikin kwanaki 14, kasar ta karbi maniyyata 84,000 daga kasashen duniya, inda a kowace rana ake karbar akalla mutum 6,000.

Kimanin mutaum 210,000 suka gabatar da Umrah a rukuni na biyu cikin maniyatan.

Rukuni na uku sun fara shiga kasar ranar 1, ga watan Nuwamba, inda maniyyata daga kasashen waje suka yi Umrah tare da mazauna kasar ta Saudiyya.