Babu wanda ya tilasta ni shiga Musulunci – ’Yar fim Moji Olaiya

Ta tabbata dai shahararriyar ’yar fim daga Kudancin Najeriya, Moji Olaiya ta amshi Musulunci. Hakan ya bayyana ne a sakamakon tattaunawar da ta yi da mujallar Encomium a kwanakin baya.Kamar yadda binciken Aminiya ya tabbatar, ’yar fim din ta Musulunta tun a bara, amma aka yi ta sakaya labarin, har sai a wannan lokacin da […]

Babu wanda ya tilasta ni shiga Musulunci – ’Yar fim Moji Olaiya
Babu wanda ya tilasta ni shiga Musulunci – ’Yar fim Moji Olaiya

Ta tabbata dai shahararriyar ’yar fim daga Kudancin Najeriya, Moji Olaiya ta amshi Musulunci. Hakan ya bayyana ne a sakamakon tattaunawar da ta yi da mujallar Encomium a kwanakin baya.
Kamar yadda binciken Aminiya ya tabbatar, ’yar fim din ta Musulunta tun a bara, amma aka yi ta sakaya labarin, har sai a wannan lokacin da ta bayyana da bakinta.
Kafin Olaiya ta tabbatar da musulunta, an yi ta yamadidin cewa wai wani saurayinta ne ya matsa mata cewa sai ta amshi Musulunci. Sai dai ita kuma a nata bahasin, ta bayyana cewa babu wani mutum da ya tilasta mata ta shiga Musulunci. “Musulunci ba a shigar shi bisa tilas, sai mutum ya amince don kashin kansa.” Inji Moji, wacce ta yi fice wajen fitowa a fina-finan Ingilishi da kuma na Yarabanci.
Moji, wacce a can baya mabiyar addinin Kirista ce, ta ce: “A batun gaskiya, Musulunci addini ne na zaman lafiya. Babban abin da ya fi burge ni kuma nake sha’awa game da addinin shi ne, mutum na da ’yancin yin bauta ya gana da Ubangijinsa, ba sai ya bi ta karkashin wani Fasto ba. Ba ka da bukatar tilas sai wani ya yi maka rokon Allah. Kai da kanka za ka iya ganawa da Ubangiji Allah mai girma ba tare da wani shamaki ba, ka roke shi dukkan bukatarka a duk lokacin da kake so kuma Ya amsa maka. Ina yin ibada tun daga ranar da na amshi addinin Musulunci kuma ina ganin tasirin haka.”
Da take ba da labarin rayuwarta kafin ta shiga Musulunci, ta ce mahaifiyarta Musulma ce, domin Alhaja ce. Daga bisani ne ta auri wani mutum Kirista, wanda dalili ke nan ita ma daga bisani ta canza zuwa addinin mijin nata.
’Yar wasan kuma ta ce ba ta jin dadin yadda mutane ke ta yada jita-jitar cewa wai wani saurayinta ne ya matsa mata ta Musulunta. “Wannan ita ce matsalar da nake fuskanta daga mutane, idan ka ce kana yin wani abu, sai su ce dole akwai wani namiji da ya matsa maka ka yi shi. To ni dai babu wani namiji da ya zama dalilin shiga ta Musulunci. Na sha fadin cewa tun asali mahaifiyata Musulma ce, daga baya ne ta zama Kirista, amma na dade ina sha’awar addinin Musulunci. Na taso rayuwata tsakanin Musulunci da Kiristanci amma a lokacin nan ne na yanke hukuncin shiga Musulunci dari-bisa-dari kuma ba na yin nadamar yin haka ko kadan.” Inji Moji Olaiya.