Gaskiyar batun garkuwa da Sheikh Bello Yabo
Sheikh Bello Yabo ya kuma ƙaryata labarin cewa hukumar DSS ta kama shi
Sheikh Muhammad Bello Yabo, fitaccen malamin Musulunci a Jihar Sakkwato, ya ƙaryata rade-radin da ke yawo cewa ’yan bindiga sun yi garkuwa da shi.
A hirar ta musamman da wakilinmu ya yi da shi, Sheikh Bello Yabo, ya bayyana cewa babu ƙamshin gaskiya kuma a labarin da ke hukumar DSS ta tsare shi.
Fitaccen malamin ya shaida wa wakilin Aminiya ta wayar tarho cewa, “babu ɗan bindigar da ya yi garkuwa da ni,” kamar yadda ake yaɗawa.
Sheikh Bello Yabo ya ce, “tun makon da ya wuce na ji ana yaɗa cewa ’yan ta’adda sun yi garkuwa da ni.
- Ambaliya ta raba dubban mutane da gidajensu a Maiduguri
- DSS ta sako Ajaero ’yan mintoci kafin cikar wa’adin NLC
“Mutane da dama daga nan Sakkwato da ma wasu ƙasashe sun yi ta kira na suna tambayae gaskiyar maganar an yi garkuwa da ni.
“Ka san yanzu zamani ne na Soshiyal Midiya, inda miyagun mutane ke yawan yaɗa irin waɗannan raɗe-radin
“Da farko cewa aka yi ’yan ta’adda sun yi garkuwa da ni, daga baya kuma aka ce hukumar DSS ta kama ni.
“Wannan duk ji-ta-ji-ta ne. Yanzu da muke maganar nan da kai ina gida tare da iyalina.
“Babu ɗan bindigar da ya yi garkuwa da ni, kuma DSS ba ta tsare ni ba.
“Ina kira ga jama’a, musamman malaman Musulunci cewa a koyaushe su riƙa tantance sahihancin duk abin da aka kawo musu, kafin su bayyana wa mabiyansu.
“Yin hakan na da muhimmanci matuƙa,” in ji malamin.