Babu wanda zai iya mayar da Najeriya kasar Musulunci – Janar Buhari

Tsohon Shugaban kasa kuma mai neman takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu wani mutum da zai iya mayar da Najeriya kasar Musulunci.Buhari ya fadi haka ne a Fatakwal ranar Larabar da ta gabata, a yayin da yake kamfen na neman wakilan jam’iyyarsa ta APC su amince da […]

Babu wanda zai iya mayar da Najeriya kasar Musulunci – Janar Buhari
Babu wanda zai iya mayar da Najeriya kasar Musulunci – Janar Buhari

Tsohon Shugaban kasa kuma mai neman takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu wani mutum da zai iya mayar da Najeriya kasar Musulunci.
Buhari ya fadi haka ne a Fatakwal ranar Larabar da ta gabata, a yayin da yake kamfen na neman wakilan jam’iyyarsa ta APC su amince da shi. Ya ce mutanen da suke yi masa yarfen cewa shi mai tsattsauran ra’ayin Musulunci ne, suna yin haka ne da gangan, da nufin bata masa suna. Ya bayyana cewa Najeriya kasa ce mai mabambantan kabilu da addinai daban-daban, wanda da wuya wani mutum ya ce zai tilasta wa al’umma su bi addini daya kacal.
Shi ma Gwamnan Jihar Ribas, Chibuike Amaechi ya karyata jija-jitar da ake yadawa, inda ake cewa wai duk wani dan jam’iyyar APC Musulmi ne. “Masu yarfe ne a siyasance suke cewa jam’iyyar ACP wai Jam’iyyar Musulunci ce, wanda hakan ba gaskiya ba ne. “Inji gwamnan.
Amaechi ya fadi haka ne a yayin da yake ganawa da daliban Jami’ar Ilimi ta Ignatius Ajuru a Fatakwal. Ya jaddada cewa APC ba Jam’iyyar Musulunci ba ce kuma ba ta da niyyar tursasa wa kowa ya zama Musulumi a Najeriya idan ta ci zabe a badi.
Ya kuma wanke Janar Buhari daga wannan jita-jita, inda ya jaddada cewa APC jam’iyya ce ta mutane masu son kawo ci gaba ga al’ummar Najeriya. “APC ba Jam’iyyar Musulunci ba ce, domin kuwa lokacin da Janar Muhammadu Buhari (ritaya) yake shugabancin kasa, lokacin yana da kuruciya bai mayar da Najeriya kasar Musulunci ba kuma idan ma a yanzu yana son yin haka sai ya samu goyon bayan Majalisun Tarayya, inda dole sai an tafka muhawara kan batun. Buhari ba zai mayar da Najeriya kasar Musulunci ba, kada ku damu da abin da magabtan siyasa ke cewa.” Inji Amaechi.
Ya ci gaba da cewa: “Ni kaina cikakken Kirista ne mabiyin darikar Katolika kuma ina bautar Allah sosai. Ba gaskiya ba ne da ake cewa APC za ta musuluntar da Najeriya. Shi kansa Shugaban APC na kasa, Mista John Oyegun, mabiyin addinin Kirista ne, matar Bola Tinubu, Kirista ce, mai dafa wa Buhari abinci, Kirista ne kuma dan kabilar Ibo ne, direbansa ma Kirista ne. A matsayinsa na shugabansu, duk Kiristocin da ke aiki a gidansa yana ba su hutu a ranar Lahadi domin su je bautar Allah a Coci. Don haka babu wani da zai amince da abin da abokan adawar mu suke fadi game da Buhari.”

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi