Babu wanda zai kwatanta lokacin da Buhari ya karbi mulki da yanzu – Danladi Pasali
Alhaji Danladi Garba Pasali shi ne Shugaban Kungiyar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Muhammad Buhari ta (BCO), kuma shi ne Sakataren Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya, a tattaunawarsa da wakilinmu, ya ce babu wanda zai kwatanta yanayin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karbi mulkin kasar nan da wannan lokaci da muke ciki: […]
Alhaji Danladi Garba Pasali shi ne Shugaban Kungiyar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Muhammad Buhari ta (BCO), kuma shi ne Sakataren Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya, a tattaunawarsa da wakilinmu, ya ce babu wanda zai kwatanta yanayin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karbi mulkin kasar nan da wannan lokaci da muke ciki:
Me za ka ce kan maganganun da wadansu ke yi, cewa al’ummar Arewa ba su amfana da gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba?
Wato abin da nake son ka gane ba a taba gwamnatin dimokuradiya da babu ’yan adawa ba. Kuma dan adawa yana da ’yancin ya fadi komai. Misali wani dan adawar ko Aljanna ka kai gidansa, zai ce maka ba Aljanna ba ce. Don haka shi dan adawa duk abin da ka yi ba ka yi daidai ba.
Abin da nake so jama’a su gane shi ne, babu yadda za ka kwatanta lokacin da Shugaba Buhari ya karbi mulkin kasar nan, da wannan lokaci da muke ciki. Ya kamata mu tuna lokacin da ba ma iya zuwa masallatai da coci da kasuwanni da tashoshin mota, saboda bama-baman da suke tashi. A lokacin mutane suna ganin kamar kasar nan za ta wargaje. Hatta albashi yana neman ya gagari akasarin jihohin kasar nan. Don haka idan mutum ya tuna wancan lokaci, ya ce ba a samu wani canji ba, a Arewa ko Najeriya ya fadi son ransa ne kawai.
Kuma zuwan Buharin nan, ga shi an farfado da aikin masana’antar mulmula karafa ta Ajaokuta da fara aikin hako mai a Arewa, an cire makudan kudade don wannan aiki, na hako mai. Haka kuma a wannan lokaci na Buhari ne, kowa ya rungumi aikin noma a Arewa. Yanzu idan ka samu mutanen Arewa 100, za ka samu mutum 65 kowa yana kokarin ya koma gona ne. A zuwan Buhari ne, yau kowa yake cin shinkafar da ake nomawa a Najeriya. A da kafin zuwan Buhari mun dogara da shinkafar da ke shigowa daga waje ne. Don haka duk mai hankali ya san cewa Buhari ya fara sa kasar nan, kan hanya.
Kuma kamar maganar rufe kan iyakokin kasar nan da Gwamnatin Buhari ta yi, duk kasar da ka ga ta ci gaba a duniya, idan ka duba za ka ga sai da ta rufe, kan iyakokinta.
Yaya za a yi a ce kasa kamar Najeriya ba za ta iya ciyar da kanta ba? Bayan muna da kasa da yanayi da ruwa, a ce shinkafar da za mu ci sai an shigo da ita, daga waje? Don haka hana shigo da shinkafar da Gwamnatin Buhari ta yi, ba karamin alheri ba ne. Idan ka lura daga lokacin da aka rufe kan iyakokin kasar nan, an samu gagarumar nasara wajen sha’anin tsaro, domin an samu raguwar hare-haren da ake kaiwa garuruwan kasar nan.
Haka ta wajen harkar man fetur, ’yan kungiyarmu ta dillalan mai, akalla an rufe wa ’yan kungiyarmu gidajen mai sama da dubu biyu, sakamakon rufe kan iyakokin kasar nan. Amma mun tsaya mun fadakar da ’yan kungiyarmu cewa gwamnati, ba ta yi wannan abu don ta tursasa wa mutane ba ne. Domin idan aka lura daga lokacin da aka rufe iyakokin zuwa yanzu, man da ake sha a kasar nan ya ragu da kusan kashi 30 cikin 100.
A da kashi 30 din nan, ana fitar da shi ne zuwa waje, kuma Najeriya tana biyan kudaden tallafi na wannan mai da ake fitarwa. Don haka duk wadannan abubuwa ne da suke nuna cewa, an samu ci gaba a kasar nan.
Yanzu idan ka je gidajen dafa abinci, za ka ji kowa yana neman shinkafar gida ce. Dama wannan kishin kasa Buhari yake son cusa wa ’yan Najeriya. Kuma wannan kishi ya fara shiga zukatan ’yan Najeriya.
Me za ka ce kan cin bashi da Gwamnatin Buhari ke kokarin yi daga waje?
Babu kasar da za ta ci gaba ba tare da ta ci bashi ba, domin da bashi ake gina kasa. Kasar Amurka da muke cewa ita ce babbar kasa a duniya, ta fi kowace kasa yawan bashi a duniya. Don haka duk wani bashi da za a ciwo wanda zai agaza wa kasa wajen ci gabanta daidai ne. Duk abin da wannan gwamnati za ta yi, wanda zai taimakawa kasar nan, daidai ne a yi shi. Don haka ya yi daidai a karbo wannan bashi, don a bunkasa harkokin kasuwanci da masana’antu, ta yadda za a samar wa matasa ayyukan yi.
Yanzu a Najeriya babu gidan da babu matasan da ba su da aikin yi. Don haka samar da masana’antu da masu zuba jari ne, zai warware mana wannan matsala, ta rashin aikin yi. Yanzu ba gashi ba, da bashin da aka ciwo ne ake ta yi mana aikin hanyoyin jiragen kasa da hanyoyin mota a Najeriya.
Wadansu sun fito sun cewa Buhari yana son ya yi tazarce, me za ka ce kan masu wannan magana?
Marasa kishin kasa ne suke irin wadannan maganganu. Kuma don ba su san wane ne Buhari ba, shi ne ya sa suke wadannan maganganu. Buhari kan maganar bin ka’ida, ya sa talakawan kasar nan suka fito suka zabe shi. Saboda shi mutum ne mai gaskiya da amana da bin ka’ida. Don haka duk masu wannan magana, mutane ne wadanda ba sa son zaman lafiya a Najeriya. Buhari ya fito da kansa ya karyata wannan magana. Ya ce ko kwana daya ba zai kara ba a kan kujerar mulkin Najeriya.
Wane sako kake da shi zuwa ga al’ummar Najeriya?
Sakona ga al’ummar Najeriya shi ne mu ci gaba da yi wa Najeriya addu’a kuma mu ci gaba da yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari addu’a. Kuma ya kamata ’yan Najeriya su sani cewa wannan gwamnati ta Buhari, ba gwamnatin soja ba ce. Don haka Buhari yake bin ka’ida tare da taka-tsantsan wajen bin doka don gudanar da aiki.