Babu wani abin ɗauka a jawabin Tinubu — Gwamnan Bauchi

Babu wani abin ɗauka a cikin jawabin da Tinubu ya yi wa ‘yan Nijeriya.

Babu wani abin ɗauka a jawabin Tinubu — Gwamnan Bauchi

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed

Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ce jawabin da shugaban ƙasar ya yi a ƙarshen makon da ya gabata, fankon jawabi ne da babu wani abin ɗauka a cikinsa.

Sanata Bala ya fadin haka ne yayin da yake jawabi a lokacin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen jam’iyyar PDP a zaɓen ƙananan hukumomin jihar.

Ana iya tuna cewa a Lahadi da ta gabata ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa al’ummar ƙasar jawabi, inda a ciki ya yi kira ga masu zanga-zangar tsadar rayuwa a ƙasar su jingine ƙudurin nasu tare da rungumar hanyoyin tattaunawa.

A cewar gwamnan na Bauchi, “na saurari duka jawabin shugaban ƙasar cikin nutsuwa da kunnen basira, amma babu komai a cikin a jawabin nasa.

“Bai [Tinubu] amince da yanayin da ake ciki ba, bai magance abubuwan da suka haifar da matsalolin ba.

“Musamman mu a nan Arewa, yana da da kyau mu tashi mu farga mu fahimci cewa lallai akwai bacin rai da yunwa.

“Dole mu fada da babbar murya cewa akwai bukatar samar da shugabanci nagari da mutunta jama’a.

Sanata Bala ya kuma bayyana cewa yana da kyau Gwamnatin Tarayyata ta fahimci cewa manufofin da take ɓullo da su ba sa aiki.

Ya ce ya kamata Gwamnatin Tarayya ta daina fakewa da bai wa ’yan Najeriya uzuri domin duk shirye-shirye ko ƙudurorin da take ɓullo da su ba sa aiki.

“Manufofin Gwamnatin Tarayya ba sa aiki. Ya kamata su fahimta cewa matsalarsu da shirye-shiryensu ne ke haddasa matsalolin da ake ciki a ƙasar nan, don haka ya kamata su canja.”