Babu wani abu ’yancin kananan hukomomi – Gwamna Fayemi
A makon jiya ne jaridun Daily Trust da Aminiya suka yi tattaunawar musamman da Gwamnan Jihar Ekiti kuma Shugaban Majalisar Gwamnonin Najeriya, Mista Kayode Fayemi, inda ya tabo batutuwa da dama. Mun tsarkuro wasu daga cikin tambayoyin da ya amsa kamar haka: Ko kana goyon bayan ba kananan hukomomi ikon cin gashi kansu? Maganar […]
A makon jiya ne jaridun Daily Trust da Aminiya suka yi tattaunawar musamman da Gwamnan Jihar Ekiti kuma Shugaban Majalisar Gwamnonin Najeriya, Mista Kayode Fayemi, inda ya tabo batutuwa da dama. Mun tsarkuro wasu daga cikin tambayoyin da ya amsa kamar haka:
Ko kana goyon bayan ba kananan hukomomi ikon cin gashi kansu?
Maganar gaskiya matakan gwamnati guda biyu ake aiki da su a kasar nan ba uku ba kamar yadda aka sani. Na san wadansu za su iya cewa haka ne, amma ba haka yake ba. A fahimtata dangane da tsarin mulkin kasar nan, a matsayina na masanin kimiyyar siyasa, muna da matakai biyu ne kadai; tarayya da kuma jiha. Masana kimiyyar siyasu sun ce tsarin kirkiro kananan hukumomi sharar fage ce na tsarin raba karfin iko. Lokacin da muka fara yunkurin shigo da tsarin kananan hukumomi a karkashin Kwamitin Dasuki a 1976, za ka iya cewa an ba mu umarni ne kawai mu yi. Akwai kura-kurai da yawa ta yadda sojoji suka zauna suka zayyana kananan hukumomin. Kawai an yi la’akari da waye yake kusa da gwamnati, ko yake da alaka da ita, ba tare da bin ka’ida ba. Haka hedkwatocin kanan hukumomin ma ba a bi ka’idojin da suka kamata ba wajen samar da su.
Za ka iya cewa jihohi ma a haka aka fitar da su, amma bambancin shi ne akalla an yi amfani da wasu ka’idoji da suka dace wajen fitar da jihohi, kamar maganar fadin kasa, yawan jama’a da kabilu da sauransu. Babbar matsalar da nake ganin ta fi addabar kananan hukumomi ita ce, ba mutanenmu ba ne suka samar da su. Ina ganin mun kai wani mataki da ya kamata a ce kananan hukumomi sun zama wani yanki daga cikin jihohinmu, ta yadda za su zamo karkashin jihohin. Idan za a samu kananan hukumomi 50 a jiha, zai zamo abu mai sauki a wurin jihar nan ta kula da gudanar da su. Zai zamo kowace jiha ita za ta kula da kananan hukumominta, wato za su zamo karkashin ikon jiha. To amma inda matsalar ta samo asali shi ne ta yadda kudaden kananan hukumomi da na jihohi suke zuwa daga Gwamnatin Tarayya, har ma wadansu suna ganin ya kamata a rika ba kananan hukumomi kudadensu kai-tsaye ba tare da sun bi ta wajen jihohi ba.
A takaice dai ba ka goyon bayan ba kananan hukumomin ’yanci?
Babu wani abu kamar ’yancin kananan hukomomi
Amma akwai kason kudinsu daga Gwamnatin Tarayya. Suna da shugabanni, amma ba a ba su damar su yi aiki da 0kudade kai-tsaye sai dai gwamnoni su bada umarni. Yaya abin yake?
A’a, hakan ba gaskiya ba ne.
Amma haka na faruwa a wasu jihohi?
A’a. Ban san jihohin da kake magana ba. Amma ka zo Jihar Ekiti ka gani, muna da kananan hukumonmi. Kai ko kafin ma in zama Gwamna an riga an yi zaben kananan hukumomi a nan. Don haka ko da na shigo na tarar da su suna aikinsu, kuma dukkansu daga jam’iyyar adawa suke. Amma haka na yi aiki da su har shekara daya kafin mu sake sabon zabe. Kuma ban taba rike musu ko anini ba.
Ana ina cewa akwai tsari mai kyau a wannan hanyar da ake bi yanzu. Amma kuma ba na goyon bayan tsarin da ke shataletale, inda Gwamnatin Tarayya ke zagaye gwamnatocin jihohi tana tura wa kananan hukumomi kudinsu kai-tsaye tunda dai duk suna karkashin jihohin ne. Ni a wajena wannan shi ne tsarin shataletale.
Wacce hanya ce mafi sauki ta tafiyar da wannan tsari?
A zahirin gaskiya, dole ne mu canja tsarin kananan hukumomi ta ba jihohi damar rage su zuwa yawan da kowace jiha za ta iya daukar nauyinsu. In dai har ana son a daidaita aljihun gwamnati.
Wannan na nufin a kara wa gwamnoni karfi?
Ba dole sai an yi haka ba, ban ce dole gwamnoni su rike wuka da nama ba. Ka ga a tsarin da yake a cikin Kundin Tsarin Mulkin Kasa a yanzu, jihohi su ke rike da kananan hukumomi, don haka yaya muke yaudarar kanmu? Duk abin da za a ba kananan hukumomi sai ya bi ta hannun jihohi. Kuma idan ka karanta Sashe na 162 na Kundin Tsarin Mulkin Kasa, za ka ga ya yi cikakken bayani. Wannan shi ne dalilin da ya sanya Kungiyar Gwamnoni ta kai Hukumar NFIU gaban kotu muna kalubalantarta kan dagewar da ta yi na sai dai a tura wa kananan hukumomi kudinsu kai-tsaye cikin lalitarsu, wanda yin hakan ja ne da Kundin Tsarin Mulkin Kasa. A halin yanzu dole a bi abin da ya fada, tunda ba a riga an yi masa wata kwaskwarima ba kamar yadda wadansu suke ta kiraye-kiraye.
Ka ce sojoji ne suka kirkiri kananan hukumomi, to amma su ma jihohin soja ne suka kirkire su, ko wannan na nufin ba ka gamsu da wannan tsarin da ake bi a yanzu ba?
Maganar gaskiya ita ce, akwai matsala a tsarin jihohi da muke bi yanzu. Kuma wannan shi ne dalilin da ya sanya nake goyon bayan a ba kowane bangare na kasar nan kwaryakwaryar ’yanci. Ai ka ga abin da muka fara yanzu a yankin Kudu masu Yamma.
Amotekun?
Kafin wannan ma, ni ne na fara kirkiro Kungiyar Debelopment Agenda For Western Nigeria(DAWN). Ni dama can a koyaushe na yarda da hada karfi da karfe waje guda don tunkarar abubuwan da za su kawo ci gaba. Duk da yake ba kowa ke da irin wannan tunani ba. Akwai masu tunanin cewa har yanzu ma muna bukatar karin jihohi, wadanda wannan ni a ganina ba daidai ba ne. Amma ba za mu iya yin abubuwan da suka kamata ba har sai mun rage wadanda muke da su a yanzu, domin ni a nawa gani jihohin da muke da su a yanzu sun fi yawan abin da ake bukata a Najeriya.
Me ya sanya kuka kaddamar da Kungiyar Tsaro ta Amotekun duk da cewa ’yan sanda su ne gwamnati ta dora wa aikin kula da tsaro a cikin gida? Ta yaya Amotekun ta shiga aikin ’yan sanda?
Ba ka da masaniyar cewa mutane na tsoron kada gwamnoni su rika amfani da ita wajen musguna wa masu hamayyar siyasa?
Idan mutane na son kujerar Gwamna ne to su yi takara ba wai su buge wajen cewa suna tsoron za a musguna musu ba. Shin ita kanta Gwamnatin Tarayya ba ta yin amfani da ’yan sanda wajen musgunawa? Ni na san abin da ya faru da ni a zaben shekarar 2014. Je ka duba tarihi, a wancan lokaci ni ne Gwamna kuma ina da kariya, amma a haka aka muzanta ni ta amfani da ’yan sanda. Don haka kowane irin ’yan sanda za a iya amfani da su wajen musguna wa wadansu.
Ta yaya kake ganin ’yan sandan yankuna za su yi aikinsu ba tare da matsala ba?
Wannan kungiyoyi sun samo asali ne daga yadda abubuwa musamman a fannin tsaro suka sukurkuce a jihohi. Kuma kasan abu mafi muhimmanci a cikin ayyukan Gwamna shi ne ya tabbatar da tsaro da ci gaban jama’arsa kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya nuna.
Mutanen da suke karkashinmu a koyaushe suna cewa ba mu san abin da kuke yi ba, kullum kuna saya wa ’yan sanda motoci da kayan aiki kuma kuna ba su alawus amma kullum abubuwa kara tabarbarewa suke yi.
Babu wani sabon abu a cikin wannan shiri namu, na ji dadin kalaman wadansu gwamnonin Arewa ta Tsakiya, na karanta a jarida yadda Gwamnan Jihar Filato Lalong ya ce ya gamsu da irin shirin da muka yi a Kudu masu Yamma. Kuma su ma suna da irin wannan tunani. Don haka Amotekun ba wani abu ba ne sabo illa dai muna son mu sanya jama’armu cikin harkar tsaron gida. Kuma ko da ’yan sanda suna maraba da sanya jama’a cikin harkar tsaro
Amma kuma su ne za su bayar da horo?
Za a iya cewa haka, amma dai ai ana sanya jama’a ne a cikin harkar tsaro a tafi tare don cimma buri. Kai babu fa wani abu sabo da muka zo da shi wanda a baya ba a yin sa. Misali kun ruwaito a cikin jaridarku kuna nuna yadda Gwamna Zulum yake mika wa soja da ’yan sanda da kuma ’yan sa-kai motoci. Me ake nufi da ’yan sa-kai? Na san ka san abin da ’yan sa-kai ke nufi? Kuma mene ne ya sanya ’yan sa-kai suke da tasiri a Arewa maso Gabas ? Domin su suka san kasar yankinsu sako da lungu kuma su suka san jama’arsu don haka sun fi kowa sanin yadda za a tunkari wuraren. Boko Haram ba daga wata duniya suke ba, ’yan Najeriya ne kuma suna nan ana tare da su cikin jama’a. Don me za mu rika yaudarar kanmu? Don haka abin da muke yi a Kudu maso Yamma bai saba wa doka ba. In an ce ana tsoron kada a yi amfani da su wajen musguna wa abokan hamayya wannan ba hujja ba ce. Shi ya sanya aka bar Amotekun a matakin yanki ba na jiha ba.
Amma akwai gwamnonin da ba su halarci taron kaddamarwar ba, wannan na nufin ba sa goyon bayan shirin dari bisa dari?
Kowane Gwamna yana ciki, ba abu ne da muka yi rana tsaka ba, shiri ne da muka fara tun watan Yulin bara lokacin da muka lura an fara kama jama’a don neman kudin fansa da kuma sace -sacen shanu. Kowane Gwamna ya sanya hannu kuma ya aiko da mota da ya ba su zuwa Ibadan. Ko a ranar 10 ga Janairu ina tare da Gwamna Babajide San-Olu kuma ya yi kokarin zuwa taron amma hazo ya hana jiginsa tashi. Don haka shi kadai ne Gwamnan da bai zo ba kuma bai turo Mataimakinsa ba saboda wannan matsala.
Kana jagorantar wata babbar murya da gwamnati ke sauraro wajen aiwatar da wasu kudirorinta, ko ba ka ganin wannan wata dama ce da ta kamata ku yi aiki hannu da hannu da Gwamnatin Tarayya?
Muna aiki tare, watakila sai in ba ka bayani, watakila ba ka san ni ne ke Shugabantar Karamin Kwamitin Tsaro na Kwamitin Tattalin Arziki na Kasa (NEC) ba. ’Yan sanda a gaskiya suna kokari
Ganin cewa Najeriya kasa ce mai yawan jama’a, miliyan 200 kuma ba mu da yawan ’yan sanda da suka kai dubu 400 kuma a hakan akwai kimanin dubu 150, daga cikinsu da suke tsaron manyan mutane, to me muke magana kuma? Komai kwazon ’yan sanda babu yadda za a yi a ganshi. Wannan shi ne ya kawo maganar sanya mutane cikin harkar tsaro.
Kuma a taronmu na Ibadan mun fayyace komai, kamar ni a jihata ai da duk jami’an tsaro muke aikin nan, akwai ’yan sanda da ’yan sandan farin kaya da kwamandan soja da sauransu, don haka in ka zo Ekiti, babu wani shiri na Amotekun da muke yi ba tare da sanin jami’an tsaro ba.
Akwai jita-jitar da ake yadawa, wadansu na cewa wai sun ga hotonsu rike da bindiga. Me ya sa za su rike bindiga?
Dalilin kafa su shi ne su rika samar wa sauran jami’an tsaro da muhimman bayanai. Ko su kama masu laifi, wannan kuwa hakki ne da ya rataya a kan kowa ma. Kama mai laifi ka mika wa jami’an tsaro. Ban san me ya sanya ake ta cece-ku-ce ba. Kowa ya san halin da kasar nan take a fagen tsaro, kai ko Shugaban ’Yan sandan kasa ya fadi haka. Na san hi a matsayin jami’i mai kwazo da son gaskiya tunda na yi aiki da shi a lokacin da na yi Gwamna karo na farko. Yana da ra’ayin sanya jama’a cikin harkar tsaro. Ka je ka tambaye shi zai fada maka muna kan hanya.