Babu wani hari da aka kai sakatariyar NUJ a Yobe — ’Yan Sanda
Rundunar ta ja hankalin ‘yan jarida kan tabbatar da sahihancin labari kafin wallafawa.
Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, ta ƙaryata rahotannin da ke nuna cewar an kai hari sakatariyar ƙungiyar ’yan jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Damaturu.
Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Juma’a.
- An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe
- Wata mata ta ƙona al’aurar ’yarta da wuta kan zargin maita a Bauchi
Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce abin da ya faru shi ne wani jami’in tsaro da ke gadin wajen ne ya samu rauni a ƙafarsa ta hagu.
A cewarsa, raunin ba shi da alaƙa da harbin bindiga, kamar yadda wasu shafukan Internet suka wallafa.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:45 na daren ranar 19 ga watan Satumba, 2025.
Rundunar ta ce babu wani ɗan jarida ko ma’aikacin NUJ da aka kai wa hari ko aka yi wa barazana.
SP Abdulkarim, ya ƙara da cewa ana ci gaba da bincike kan lamarin, kuma ya bai wa jama’a tabbacin cewa za a ɗauki matakan da suka dace.
Rundunar ta kuma yi kira ga ’yan jarida da su guji yaɗa labarai ba tare da tabbatarwa ba, domin hakan na iya haifar da tashin hankali.