Babu wani sabo abu a nada sanata sheriff shugaban PDP
Daga dukkan alama zuwa yanzu jam`iyyar PDP, da ta yi mulki kasar nan har tsawon shekaru 16, bayan an dawo mulkin dimokuradiiya a shekarar 1999, ta fara shawo kan rikicin shugabancin da ta dade tana fama da shi, musamman na baya-bayan nan, baya-bayannan da ya biyo zaben tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff, […]
Daga dukkan alama zuwa yanzu jam`iyyar PDP, da ta yi mulki kasar nan har tsawon shekaru 16, bayan an dawo mulkin dimokuradiiya a shekarar 1999, ta fara shawo kan rikicin shugabancin da ta dade tana fama da shi, musamman na baya-bayan nan, baya-bayannan da ya biyo zaben tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff, wanda kungiyar Gwamnonin Jam`iyyar suka yi uwa da makarbiya cikin Kwamitin Zartarwar jam`iyyar kasa baki daya wajen ganin an zabe shi. Bayan kada kuri`a daga cikin mutane 71, Sanata Sheriff, ya samu kuri`a 60. Zaben da har zuwa wannan lokaci Kwamitin Ministocin PDP da ke karkashin shugabanci Alhaji Tanimu Turaki ke adawa da shi.
Tun a watan Mayun bara, bayan jam`iyyar PDP ta fadi babban zaben kasar na shekarar da ta gabata, matsin lamba ya yi yawa a kan shugaban jam`iyyar, kuma tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Alhaji Ahmed Adamu Mu`azu, a kan lallai tunda ya yi sanadiyar faduwar jam`iyyar a babban zaben (bayan ta shafe shekaru 16, tana mulkin kasar nan), to, ya sauka, ya kuma saukan. Jam`iyyar PDP din ta afka cikin rikicin shugabancin da ba ta taba gani ba. Bayan Alhaji Adamu Mu`azu ya sauka ne ya mika ragamar mulkin jam`iyyar ga mukaddashinsa Cif Uche Secondus. Tsarin mulkin PDP din ya tanadi cewa, idan shugaba bai kammala wa`adinsa ba a bisa ga wani dalili mai karfi, to, sai a zabo wani daga shiyyar da ya fito don ya kammala wa`adin. Ta haka ne Alhaji Adamu Mu`azu ya gaji Alhaji Bamanga Tukur, da suka fito daga shiyya daya ta Arewa maso Gabas, Alhaji Bamangan da a wancan lokacin shi ma gwamnonin jam`iyyar PDP din suka kafa masa kahon zuka sai da ya sauka, ya kuma sauka bakatatan.
Jinkirin nada wanda zai gaji Ahmed Mu`azu daga shiyyarsa ta Arewa maso gabas ya sanya Barista Ahmed Gulak tsoho nmashawarci a kan harkokin siyasa ga tsohon Shugaba kasa Jonathan, ya sanya ya garzaya wata babbar kotun Abuja yana neman sai ta haramta rikon shugabancin jam`iyyar da Cif Secondus, yake yi bisa ga cewar hakan ya karya ka`ida, kuma ta bayyana cewa, wani daga waccan shiyya ya kamata ya ja ragamar shugabancin jam`iyyar, har zuwa lokacin da shiyyar za ta kammala wa`adinta. Haka din aka yi, Kotun, ta amince da rokonsa, hukuncin da har ya ba Barista Gulak din damar ya yi shelar bayyana kansa a zaman shugaban jam`iyyar.
Da aka kai ga wannan matsayi, sai ya sanya iyayen jam`iyyar da shugabanninta da sauran masu ruwa da tsaki, musamman wadanda suka fito daga shiyyar Arewa maso Gabas suka himmatu wajen ganin lallai an nada, dukkan wanda za a nada don girmama hukuncin Kotun. Haka ta sa a wani hadadden taron Kwamitin zartarwar jam`iyyar aka bayyana sunan Alhaji Modu Sheriff, a matsayin sabon shugaban jam`iyyar, bayan an kada kuri`a, inda a cikin mutane 71, da suka halarci taron, 60 suka kada masa kuri`ar zabensa, 11 kuma suka ki zabensa. A tsarin mulki irin na aiki da ra`ayi jama`a, ko tantama, babu, Sanata Sheriff, ya ci zabe. Amma kuma a gefe daya sai tsofaffin Ministocin PDP, a karkashin dandalinsu da tsohon Ministan Ayyuka na musamman Alhaji Tanimu Turaki, suka yi wani taro suka ce Allah Ya kashe su, ba su amincewa da shugabancin Sanata Sheriff, haka shi ma Kwamitin riko na Amintattun jam`iyyar na kasa baki daya a karshin Shugabancin Sanata Walid Jibrin ya ce ba da shi ba. Dukkan su hamzari iri daya suka bayar na cewa ba a bi ka`ida ba, kuma wai Sanata Shariff ba shi da kima da mutuncin da zai kai jam`iyyar tudun mun tsirar da take bege na dawowa a kan karagar mulkin kasar nan a babban zaben shekarar 2015.
karewa ma da karau tsohon Ministan kula da zirga-zigar jiragen sama Mista Femi Fani-Kayode, har zargin Sanata Sheriff ya yi da shi ne babban mai tallafa wa kungiyar Ahlis Sunnah Lid-Dawati Wal jihad da aka fi sani da Boko Haram, `yan kungiyar da ake ta dauki ba dadi da su yau kusan shekaru bakwai, dauki ba dadin da ya yi sanadiyar kashewa da jikkata daruruwan mutane da kona dukiyoyin mahukunta da na al`umma, musamman a jihohin Borno da Yobe da Adamawa da Gwambe, baya ga sace `yan matan Sakandaren garin Chibok da ke cikin Jihar Borno, yau kwanaki 690. Zarge-zargen da sabon shugaban jam`iyyar PDP din ya musanta, har ma yana kafa hujjar da cewa daga cikin wadanda `yan Boko Haram din suka kashe zuwa yanzu, har da dan uwansa, bayan shi kansa a kan barazanar za su kashe shi yake har gobe.
Yanzu dai maganar da ake ciki, ita ce tuni Sanata Jibrin ya bayyana cewa, Kwamitin amintattun jam`iyyar ya sanya giyar ribas, ya dawo yana goyon bayan shugabancin Sanata Sherif, bisa ga amincewar da aka yi na cewa, wa`adin Sanata Shariff zai kare a watan Maris mai kamawa zai shugabanci jam`iyyar ne na tsawon watanni uku kawai, wato zuwa watan Mayu mai zuwa, wanda a cikin wannan tsakanin ne za a gudanar da taron zaben shugabannin jam`iyyar tun daga mazabu zuwa kananan hukumomi zuwa jihohi zuwa shiyya-shiyya zuwa kasa baki daya, wanda za a fito da cikakken bayanai a kan yadda za a gudanar da tarurrukan nan da makonni biyu masu zuwa in Allah Ya kai mu. Amma kuma su tsofaffin Ministocin PDP, suna can sun ci gaba da hawa dokin naki akan shugabancin Sanata Shariff, kamar yadda shugaban dandalin Alhaji Tanimu Turaki ya shaida wa `ya`yar wannna jaridar ta ranar Lahadin da ta gabata, wato Daily Trust Sunday, 28-02-16. Ko da yake ya tabbatar da cewa, shirye suke da a ci gaba da tattaunawa don neman mafitar kai jam`iyyar tudun mun-tsira, musamman samun nasararta a zabubbukan 2019, in Allah Ya kai mu.
A cikin wannan hayani abin da ya tabbata shi ne kungiyar Gwamnonin PDP, su suka yi uwa da makarbiya wajen tabbatar da nada Sanata Sheriff a kan wannan kujera, kamar yadda suka saba, tunda jam`iyyar PDP ta zo kan karagar mulki a shekarar 1999. Idan mai karatu bai manta ba a zaben fidda gwanin neman takarar shugabancin kasa na PDP don zaben shekarar 2003, da aka yi a Jos, mataimakin shugaban kasa na wancan lokacin Alhaji Atiku Abubakar, ya yi amfani da gwamnonin jihohi wajen tilasta wa Shugaba Obasonjo a kan lallai sai in ya amince zai tafi da Atikun kana za su sake tabbatar masa da takarar. Haka kuwa aka yi, yana furta ya yarda, gwamnonin jihohi suka umurci wakilansu da su zabi Obasanjo. Shi kan shi tsohon Shugaban PDP Alhaji Bamanga, gwamnonin jam`iyyar sa suka sa shi gaba har Shugaba Jonathan ya amince ya sallame shi. Haka tarihin kama karya a cikin PDP ya tabbatar ana tafiyar da ita, yanzu ma wannan kama-karya Gwamnonin PDP suka yi amfani da ita wajen kawo Sanata Sheriff, tunda an ruwaito Shugaban kungiyar Gwamnonin Cif Olusegun Mimiko yana cewa, dukkan abin da gwamnonin suka yi sun yi ne da yawon jama`arsu, har yana karawa da cewa ai duk wani dan jam`iyya daga jiha ya fito.Wannan kama-karya da nuna isa, ita su ma ministocin su ke son yi.
Muddin shugabanni a cikin mulkin dimokuradiyya, ba su yarda da cewa mulki ne na jama`a kuma daga jam`a don jama`ar, to, kuwa akwai sauran aiki. Ita kanta jam`iyyar APC, mai ikirarin CANJI, zuwa yanzu ana ganin ta fada cikin wannan ji-ji-da-kai da kama-karya, don kuwa wasu membobinta a jihohi da da ma sun fara kokawa a kan irin yadda kama-karyar da aka yi musu wajen nada `yan takara, musamman gwamnonin jihohi ta fara shafarsu. Da wannann mai karatu ka ga ke nan babu wani abu sabo cikin nadin Sanata Sheriff.