Babu wani shirin mayar da Nijeriya tsarin jam’iyya ɗaya — APC

Za mu tabbatar da ci gaba da gina jam’iyyar tamu domin ta ci gaba da cin zabe a kowane lokaci.

Babu wani shirin mayar da Nijeriya tsarin jam’iyya ɗaya — APC

Sakataren Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Ajibola Bashiru ya ce, shugabannin jam’iyyar ba su da niyyar mayar da Nijeriya kasa mai tsarin jam’iyya daya, illa ganin sun gina jam’iyyar domin ci gaba da lashe zabe a kasar nan.

Ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta gabata yayin da yake jawabi ga ɗimbin magoya bayan jam’iyyar da suka halarci Sakatariyar Jam’iyyar ta Kasa a Abuja tare da nuna goyon bayansu ga Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, inda suka nemi kada ya sauka daga mukaminsa.

Ya ce, “Ba mu ce Nijeriya ta zama kasa mai bin tsarin jam’iyya daya ba.

“Amma muna tabbatar ci gaba da gina jam’iyyar tamu domin ta ci gaba da cin zabe a kowane lokaci.

“Dole ne mu tabbatar da samuwar kuɗi don samar da ilimi da kuma ababen more rayuwa ga al’umma.

“Ba ma damuwa da ’yan adawar da ba sa son ci gabanmu.

“Za mu ci gaba da goyon bayan shugabanmu kuma jagoranmu, Shugaba Tinubu.

“Za kuma mu ci gaba da kasancewa masu haɗin kai da jajircewa a karkashin jagorancin shugabanmu na kasa, Dokta Abdullahi Umar Ganduje.

Dakatar da Ganduje da wasu kungiyoyi biyu suka yi a baya-bayan nan ya haifar da zanga-zanga, inda mutanen yankin Arewa ta Tsakiya suka yi kiran ya yi murabus.

Amma da yake jawabi ga dimbin magoya bayansa, Dokta Ganduje ya ce wadannan mutane na fargabar irin kokarin da jam’iyyar ke yi.

“Sun ji tsoro sosai saboda suna ganin a duk fadin kasar nan, babu wata jam’iyya da take yawan samun sabbabin jama’a da suke shigowa kamar jam’iyyarmu.

“Wannan yana haifar da tsoro a cikin zukatansu,’’ in ji Ganduje.

Tuni sun san 2027 tamu ce, ba su da wani katabus.

Shugaba Ahmed Bola Tinubu ne kawai in sha Allahu zai ci gaba da zama Shugaban Nijeriya.

Sai ya buƙaci magoya bayan Jam’iyyar APC su yi watsi da abin da ya bayyana a matsayin wasan yara, inda ya ce, “Mun fahimci abin da suke yi.

“Wasan kwaikwayo ne na siyasa. Abin da suke yi shi ne wasan kwaikwayo na zahiri don sun san ba su da wani abu,domin sun gaza.”