Babu wani yunkuri na musuluntar da Najeriya – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya musanta labaran da ke yawo cewa an tilasta wa yara da yawa mabiya addinin Kirista su yi karatun darusan addinin Musulunci a makarantu domin mayar da kasar mu ta Musulunci. Alhaji Sa’ad Abubakar ya yi wadannan kalamai ne a lokacin bude taron Majalisar Da’awa ta kasa […]

Babu wani yunkuri na musuluntar da Najeriya – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya musanta labaran da ke yawo cewa an tilasta wa yara da yawa mabiya addinin Kirista su yi karatun darusan addinin Musulunci a makarantu domin mayar da kasar mu ta Musulunci.

Alhaji Sa’ad Abubakar ya yi wadannan kalamai ne a lokacin bude taron Majalisar Da’awa ta kasa game da aiwatar da manufofin majalisar daga shekarana 2017 zuwa shekara ta 2025 a Bauchi, inda ya ce akwai bukatar gwamnatin ta bi abin a hankali domin kauce wa duk wani abu da zai iya kawo yamutsi ko ta da jijiyar wuya.

Ya ce addinin Musulunci addinin son zaman lafiya ne da hadin kai da yin adalci a tsakanin jama’a, sai ya gargadi wadanda ba Musulmi ba da su guji yin kalaman da za su jawo rashin zama lafiya a kasar nan.

Sarkin Musulmi ya bukaci Majalisar Da’awah ta kasa ta yada manufofin Musulunci ta hanyar fahimtarwa da lumana da yin adalci tare da kokarin ilimantar da jama’a ta yadda mabiya sauran addinai za su fahimci addinin Musulunci.

Ya ce yana da kyau a taron da majalisar za ta yi a nan gaba ta gayyaci mabiya addinin Kirista domin su zo su ji abubuwan da Musulmi ke fada da abubuwan da suke aikatawa.

Sarkin Musulmi ya roki ’yan Najeriya su kara hada kansu domin su rika warware dukan al’amuran da suka shafi kasa cikin mutunci da tattaunawa maimakon rikici ko tashin hankali.

Sai ya gargadi ’yan siyasa su guji sanya siyasa a kan abin da ya shafi rayukan mutane, su kuma dauki matakan da za a samu zama lafiya a kasar nan, inda ya yi Allah wadai da rikicin da ya faru a yankin Mambila tare da kira ga Gwamnatin Tarayya ta kafa hukumar bincike a kan al’amarin.

A jawabin Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu ya ce kiran mutane zuwa ga Musulunci da aikata ayyukan alheri umurni ne na Allah Madaukakin Sarki. Ya ce saboda haka yin kira zuwa ga addinin Musulunci hakki ne da ke wuyan kowane Musulmi, sai ya yi kira a kara tsara hanyoyin yin da’awa domin samun nasara a kokarin da ake yi isa da Musulunci ga jama’a a Najeriya.

Gwamnan Jihar Bauchi Barista Mohammed Abdullahi Abubakar wanda Mataimakinsa Injiniya Nuhu Gidado ya wakilce shi ya bukaci majalisar ta ba da gudunmawarta ta hanyar da za a kawar da ayyukan assha da rashin tarbiyya da abubuwan da suke kawo gurbacewar tarbiyya a tsakanin matasa.

Ya gode wa Sarkin Musulmi saboda yadda yake koyi da halayen Musulunci wanda yin hakan ya kara jawo hakuri da fahimta da zama lafiya da wadanda ba Musulmi ba.

Shugaban taron kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim ya ce kafa majalisar da aka yi ya dace domin hanyar da’awa ita ce hanya ingantacciya ta yada addinin Musulunci, kuma hanyar na da tsari dangane yadda za a rika gudanar da dukan ayyuka yadda ya kamata, 

Malam Ibrahim Shekarau ya roki Musulmi, musamman shugabanni su rika nuna halayen kirki da za a rika koyi da su kuma su yi kokari wajen bin koyarwar addinin Musulunci a harkokinsu.

Bako Mai jawabi Farfesa Salisu Shehu ya yaba wa majalisar saboda yadda ta fito da tsari da ake yada addinin Musulunci, sai ya roki kungiyoyin Musulmi su kara dagewa wajen yada addinin Musulunci a kasar nan. 

Shugaban Majalisar Da’awa ta kasa, Malam Muhammad Lawal Maidoki ya ce Majalisar ba ta da matsala da kokarin da ake yi na sake fasalin kasar nan in har za a bar Musulmi su samu ’yancin giggina masallatai da makaruntu a ko’ina cikin kasar nan ba tare da tsangwama ko hana su yin addininsu ba.

Ya ce “Wajibi ne a bai wa al’ummar Musulmi damar a rika  ilimantar da su a dukan makarantun da ke ko’ina a kasar nan, kuma a ba su damar yin kowane irin kasuwanci da mallakar kadarori a ko’ina a kasar nan  ba tare da nuna musu bambanci ko kai musu hari ba. Musulmi suna bukatar adalci wajen samun damar da za su shiga ayyukan soji da sauran na damara kuma a bar matansu su rika sanya sutura kamar yadda Musulunci ya tsara.”

Ya ce kiraye-kirayen ballewa daga kasa da wadansu ke yi na barazana ga zamar kasar nan dunkulalliya, inda ya bukaci a warware matsalar cikin kwanciyar hankali da natsuwa,

Shugaban ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa Fulani makiyaya a yankin Mambila, inda ya ce Fulani makiyaya ba su ce gwamnati ta yi musu hanya ko ba su ruwan sha da kayan alatu ba, bukatansu kawai burtali da labin shanu amma aka shiga yi musu kisan kare-dangi.

Ya ce lallai ne gwamnati ta fito ta yi tir da abin kuma ta kafa kwamitin binciken lamarin domin a zakulo wadanda suka tayar da fitinar a hukunta su. 

Sarakuna da malaman addini daga sassan kasar nan ne suka halarci wajen taron.

Daga bisani Sarkin Musulmi ya ziyarci fitaccen Malamin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi a gidansa inda Shehun Malamin ya yi masa addu’ar samun nasara sannan ya ba su kyautar Alkur’anai shi da Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu.

A wani labarin Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ya musuluntar da mutum uku mabiya addinin gargajiya a kauyen Miya da ke karamar Hukumar Ganjuwa a Jihar Bauchi. Mutanen sun karbi addinin Musulunci ne lokacin da Sarkin Musulmi ya je kauyen domin duba makarantar da yake ginawa a can bayan bude taron Majalisar Da’awa ta kasa a garin Bauchi.  

Mutanen yankin Miya 4,700 ne suka musulunta bayan fara kiransu zuwa ga Musulunci a baya-bayan nan.