Babu wata ɓaraka a tsakanina da Baffa Bichi — Abba Gida-Gida
Har yanzu Baffa Bichi shi ne Sakataren Gwamnati kuma muna ci gaba da yaba masa kan gudunmuwarsa.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa ya kori Sakataren Gwamnatin Jihar Abdullahi Baffa Bichi sakamakon wani taku-saka da ya shiga tsakaninsu.
Aminiya ta ruwaito cewa a halin yanzu Sakataren Gwamnatin ya shafe tsawon makonni wajen ganin likita a kasar Saudiyya, lamarin da aka umarci Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Kano, Abdullahi Musa ya ci gaba da kula da ofishinsa a matsayin mukaddashi.
- An kama buhunan takin zamani 600 na sata a Kaduna
- NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kudin Hajjin bana
Sai dai kuma tun bayan faruwar hakan ce aka rika yada rade-radi a kafafen sada zumunta musamman daga bangaren ‘yan jam’iyyar adawa cewa, an samu baraka tsakanin gwamnan da kuma sakataren gwamnatinsa.
Haka kuma, an ci gaba da yada makamanciyar wannan jita-jita bayan samun wani hadimi na musamman a Gwamnatin Kano da aka kama kan zargin yin sama da fadi da wasu kayan abinci na tallafin rage radadi, wanda kuma tuni Gwamnan ya dauki mataki a kansa.
Wasu bayanai sun ce hadimin da aka kama da wannan aika-aikar yana aiki ne a karkashin ofishin Sakataren Gwamnatin, inda ubangidansa ya tunkari gwamnan da lamarin kuma a karshe dai ba ta kwashe da dadi ba a tsakaninsu.
Sai dai da yake martani kan lamarin a wannan Talatar bayan rantsar da wasu sabbin manyan sakatarori, Gwamnan ya ce babu wata baraka a tsakaninsa da Sakataren Gwamnatin ballantana ta kai har ga batun tsige shi daga mukaminsa.
“Akwai wadanda saboda rashin sani suke yada jita-jitar cewa mun bai wa hammata iska ni da shi [Baffa Bichi], amma babu abin da za mu ce da irin wadannan mutane sai dai Allah Ya shirye su.
“Har yanzu Baffa Bichi shi ne Sakataren Gwamnati kuma muna ci gaba da yaba masa kan gudunmuwar da yake bai wa gwamnatinmu, kuma muna fatan zai ci gaba da jajircewa a kan hakan idan ya dawo.
“Duk da cewa Shugaban Ma’aikatan Gwamnati yana lura da ofishinsa saboda ba ya nan, amma hakan ba ya nufin an kore shi. Babu wanda ya sauke shi da mukaminsa.”