Babu wata guguwar sauya Ganduje da ta taso — APC

Yahaya Bello ya nesanta kansa daga neman shugabancin jam’iyyar APC.

Babu wata guguwar sauya Ganduje da ta taso — APC

Tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta musanta rade-radin da ke cewa guguwar sauya shugabanta na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ta taso.

APC na wannan gargadi ga magoya bayan tsohon gwamnan Jihar Kogi na baya-bayan nan, Yahaya Bello, da su guji neman haddasa rudani da cewa jam’iyyar tana da shugaba na kasa.

Babban Sakataren jam’iyyar na kasa, Felix Morka ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a yau Talata a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.

Aminiya ta ruwaito cewa, sa’o’i 48 da Yahaya Bello ya sauka daga mulkin Jihar Kogi inda ya damka wa sabon gwamnan da aka zaba Usman Ahmed Ododo, shafukan sada zumunta da sauran kafafen intanet sun cika da jita-jitar cewa Bellon na sha’awar kujerar shugabancin jam’iyyar.

A jiya Litinin ne dai aka ga yadda hotunan tsohon gwamnan na Kogi suka mamaye titunan Abuja har da sakatariyar jam’yyar da ke babban birnin Najeriyar.

Sai dai bayan taron babban kwamitin zartarwa na jam’iyyar, sakataren yada labaran jam’iyyar ya fito da sanarwa inda yake jaddada cewa a yanzu akwai wanda yake kan kujerar shugabancin jam’iyyar — wato tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Ya kara da cewa har yanzu Abdullahi Umar Ganduje ne shugabansu saboda haka babu maganar takarar hawa kujerar a yanzu kamar yadda magoya bayan Bello suke yadawa.

Ya ce kodayake wannan lokaci ne na dimokuraɗiyya, amma ana gargadin masu yada wadannan hotuna da su bari, domin jam’iyyar na son mayar da hankali ne a kan yadda za ta daidaita al’amuran kasa a yanzu amma ba shugabancinta ba wanda ba su da matsala a kansa.

Bayanai sun ce wasu magoyan bayan jam’iyyar APC a Arewa ta Tsakiya na ƙoƙarin ganin an tumbuke Ganduje la’akari da cewa kujerar halaliyar yankinsu ce tun bayan da Sanata Abdullahi Adamu ya yi murabus.

Ba na takarar neman kujerar Shugaban APC — Yahaya Bello 

Sai dai kuma tsohon gwamnan jihar ta Kogi, Yahaya Bello ya nesanta kansa daga wannan kamfe da ke danganta shi da neman kujerar shugabancin na APC.

Wata sanarwa da ofishin yada labarai na tsohon gwamnan ya fitar yau Talata ya zargi shugabannin hamayya da wadanda ya kira makiya a cikin jam’iyyar tasu da kitsa wannan abu domin bata sunan tsohon gwamnan.