‘Babu wata jami’a a Najeriya da ta kai ABU Zariya samar da kwararru a fannin shari’a’

Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta bayar da gudunmuwa ga ci gaban harkokin shari’a ga Najeriya.

‘Babu wata jami’a a Najeriya da ta kai ABU Zariya samar da kwararru a fannin shari’a’

Jami’ar Ahmadu Bello

Tsangayar Fannin Ilimin Shari’a ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta bayar da gudunmuwa ga ci gaban harkokin shari’a ga Najeriya tun da kafuwarta zuwa yau.

Darakta Janar na Cibiyar Ci gaban Harkokin Shari’a na Najeriya, Farfesa Muhammad Taufiq Ladan ne ya bayyana haka a kasidar da ya gabatar domin bikin cikar Jami’ar Ahmadu Bello shekara 60 da kafuwa wadda Tsangayar Fannin Ilimin Shari’a ta shirya a Babban Dakin Taro na Jami’ar da ke Samaru.

Farfesa Taufiq Ladan ya ce babu wata jami’a a Najeriya da ta kai ta Jami’ar Ahmadu Bello samar da kwararru masu yawa a fannin shari’a.

Ya bayar da misalin cewa Jami’ar Ahmadu Bello ta samar da alkalin alkalai na kasa guda 5 daga cikin 17 da aka yi, yayin da ta samar da manyan alkalan Babbar Kotun Daukaka Kara masu yawa.

Darakta Janar Taufiq Ladan ya ce Jami’ar Ahmadu Bello ta darar wa tsara domin ba ta da na biyu ta wajen samar da fitattun masana shari’a a gida da kassashen waje.

 

Sarki Bamalli a yayin gabatar da jawabi

 

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya bayyana taron a matsayin abin alfahari  saboda ya hada fuskokin da suka dade ba su sadu ba.

Sarki Bamalli ya kuma yi kira ga wadanda suka ci gajiyar Tsangayar da Jami’ar su kawo gudunmuwarsu ga ci gaban Jami’ar.

Da yake gabatar da jawabinsa, Mai Shari’a Isiyaku Bello wanda ya shugabanci taron, ya bayyana cewa Tsangayar fannin shari’a ta Jami’ar Ahmadu Bello a harkar Shari’a a Najeriya ta wuce dukkan tunani domin ta zamo tamkar ruwan darene.

Mahalartar taron a Babban Dakin Taro na Jami’ar ABU da ke Samaru

Ya ce irin wannan haduwa na da matukar muhimmanci musamman domin ganin yadda kowa zai bayar da tasa gudunmuwa kamar yadda suka ci gajiyar ta.

Tun da farko a jawabinsa, Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Kabiru Bala ya bayyana taron da cewa na waiwaye ne tare da nemo mafita bisa yanayin da Jami’ar ta tsinci kanta musamman na rashin kudi.

Kabiru Bala ya kuma bukaci tsoffin dalibai da su bayar da tasu gudunmuwar don ci gaban Jami’ar.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja