Babu wata kungiya da ta isa ta janye Dogara daga majalisa – Zaki
Tsohon dan Majalisar Wakilai daga Jihar Bauchi, Alhaji Abdurrazak Nuhu Zaki ya ce babu wata kungiya da ta isa ta janye Shugaban Majalisar Barista Yakubu Dogara domin ba sabon dan siyasa ba ne da za a yi masa barazana.Alhaji Abdurrazak Zaki ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Bauchi inda […]
Tsohon dan Majalisar Wakilai daga Jihar Bauchi, Alhaji Abdurrazak Nuhu Zaki ya ce babu wata kungiya da ta isa ta janye Shugaban Majalisar Barista Yakubu Dogara domin ba sabon dan siyasa ba ne da za a yi masa barazana.
Alhaji Abdurrazak Zaki ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Bauchi inda ya ce “Mun lura wadansu marasa kishin Jihar Bauchi da aka dauki nauyinsu domin haddasa fitina a tsakanin Shugaban kasa da ’yan Majalisar Wakilai, sun fito suna cewa za su dawo da Yakubu Dogara daga majalisa. Ya kamata su sani abu ne mai matukar wahala a dawo da sanata ko dan majalisar wakilai, kuma muna so su bayyana mana laifin Dogara.” Ya ce ya kamata Shugaba Buhari ya yi hattara da tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo domin ba ya da wani aiki a yanzu sai neman haddasa fitina a tsakanin majalisa da fadar Shugaban kasa. “Bai kamata Cif Obasanjo ya ce ’yan majalisa mutanen banza ba ne, domin shi ne ya fara lalata majalisa a lokacin da ya yi yunkurin ta-zarce karo na uku. Duk matsalolin da ake fuskata a kasar nan, Cif Obasanjo ya haddasa su domin shi ya fito da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kuma jajirce a ba shi mukamin Mataimakin Shugaban kasa. Duk lokacin da na ga Cif Obasanjo ya je fadar Shugaban kasa na san da walakin, domin ba ya zuwa waje haka kawai,” inji Zaki.