Babu wata rigimar makiyaya da manoma illa siyasa kawai – Dodo Oroji
Alhaji Muhammadu Dodo Oroji, Tsohon Shugaban kungiyar Mayyeti Allah a Abuja. A cikin wannan tattaunawar da ya yida Aminiya, Oroji, ya bayyana ra’ayinsa akan rikicin Fulani da Manoma wanda ya ce ‘yan siyasa ke hura wutar a kasar nan: Aminiya: Wane hanyoyi kuke ganin za a bi wajen magance matsalar rikici da manoma a […]
Alhaji Muhammadu Dodo Oroji, Tsohon Shugaban kungiyar Mayyeti Allah a Abuja. A cikin wannan tattaunawar da ya yida Aminiya, Oroji, ya bayyana ra’ayinsa akan rikicin Fulani da Manoma wanda ya ce ‘yan siyasa ke hura wutar a kasar nan:
Aminiya: Wane hanyoyi kuke ganin za a bi wajen magance matsalar rikici da manoma a yankunan kasar nan?
Wannan abin ban takaici ne abin tsoro kuma abin ban haushi ne. Saboda idan ka duba kullum cewa ake fulani da manoma wannan magana ba gaskiya ba ce siyasa ce. Kuma fulani da manoma sun fi shekaru 500 a Najeriya duk jihohin nan da ake wadannan abubuwa babu inda bafulatani bai wuce da dabbobinsa ba. Da Fulanin da ke nan da manoma duk tare aka taso kuma ana zaune lafiya. Babu dalilin da wani zai kashe wani ko saboda kiwo ko noma. Abin da zai warware wannan matsala dole sai gwamnatin tarayya ta dauki mataki ta hana mutane daukar doka a hannunsu. Babu yadda za a yi ka je ka kashe mutum da matarsa da dansa a zauna lafiya. Ya kamata duk wanda ya fara a hunkunta shi. Idan ana hukunta masu wannan abun da hakan bai faru ba.
Aminiya: Tun farko me za a ce ke kawo matsala?
kabilanci da siyasa ke kawo wannan matsala. Sa’a da aka yi a Najeriya Musulmi da kiristoci ba su shiga cikin abin ba. Amma idan aka kyake har gwamnati ta yi shiru ba tare da an dauki mataki ba komai na ita faruwa. Saboda haka babu dalilin wani ya kashe wani, babu dalilin ka ce wani ba zai zo cikin jaharka ba ya yi kiwo domin ba jaharka ba tunda shi ma dan Najeriya ne. dan Najeriya na da hujjar zuwa ko wacce jahar ya yi sana’arsa.
Idan kiwo ko noma ya keyi ya yi abinsa. Babu wani gwamna da aka baiwa ikon cewa wani dan jaha ba zai je jaharsa ba. Ina tabbatar maka da wannan domin babu shi cikin dokar kasa. Najeriya kasa ce ta dukkan dan Najeriya. Kiwo da noma dukka sana’a ce da kuma sayar da kaya. Yanzu mutumin kudu zai je ya yi sana’a a Sokoto mutumin Benuwai zai je ya yi aiki a otel zai kuma iya sayan fili ya Gina kuma babu wanda ya isa ya ce mai nan ba kasar ku ba ce. Wannan ba dai dai ba ne kuma siyasa ce da kabilanci kuma wannan kabilanci ba zai kai mu ko’ina ba a cikin kasar nan.
Ya kamata mu zauna lafiya kowa ya zauna a matsayinshi idan kiwo kake ka yi kiwo in kuma sana’a kake yi ka yi abinka. Amma muddin ka ce wani ba dan uwanka bane bai da ce ba. Kuma duk mai tayar da rikici cikin kasa komai matsayinshi ya kamata a hukunta shi. Saboda haka ina kira ga gwamnatin tarayya da yan Majalisu da su dauki mataki akan wannan Lamari. Yanzu abin ya zama kamar siyasa Ana ta kashe yayan fulani da yayansu a koma kwashe masu dukiyoyi duk wannan bai dace ba. Ya kamata mutum idan ya yi laifi a hukunta shi domin haka muka sani tun tasowar mu abin da muka sani shi ne kakannin mu fulani da na makiyaya duk sun zauna lafiya.
Idan har shanun makiyaya ya shiga gonar manomi sun yi barna idan har ba za’a iya sasantawa a wajen ba sai a kira Alkali akiyasta barnar domin mafulatanai ya biya shi. Domin baka da hujjar barin shanu su shiga gona su chinye sannan kuma kai manomi baka da hujjar kashe saniya ko mutum saboda an yi maka barna. Bai kamata duk wani dan Najeriya ya dauki doka a hannunshi ba ko manomi ne ko bafulatani. Kuma batun kebe shanu a wasu wurare ai wannan tun lokacin turawan mulkin mallaka akwai shi domin babu inda ba su yi burtuli ko gandun daji ba. Akwai hanyoyi da suka yi da shanu ke bi tun daga Najeriya har Nijar. Sannan daga Nijeriya har Nijar daga Ghana har Kamaru. Amma saboda siyasa duk an yanke gandun dajin su yi gona.
Aminiya: Yanzu dai Fulanin Najeriya na yin hijara zuwa kasashe makwabta ýkenan?
Ai saboda wahalar da fulani ke sha a kasar nan yanzu idan ka je Ghana duk Fulanin Najeriya ne a can. Domin shekara 50 da suka wuce babu fulani a Ghana kwatonu daga nan har suna zuwa Tsakiyar Afirka. Sannan idan ka dubi kashi 75 na Fulanin kamarun ‘yan Najeriya ne saboda an tauye su a wurin kiwo domin ba a so su yi arziki suka koma can. Misali a Taraba babu inda ake kiwo kamar Mambila kuma sun dade da kebe dabbobinsu. Ba kada wani karfi ka ce dan kazo da mukamin mulki ka ce baka San ka ga wata al’umma a wajen.
Aminiya: Ko a kungiyance wacce shawara kuke baiwa gwamnati ta yadda za a magance matsalar?
Bari in fada maka gaskiya duk wannan abin siyasa ce kawai in ba haka ba shekaru dari biyar da suka wuce ina Fulanin da manoman dake nan kasar. Suna nan domin kowa yasan inda yake kiwo da kuma noma. Duk wanda ya dauki doka a hannunshi gwamnatin tarayya ta hukunta shi ko wanene. Babu dalilin wani ya kashe wani.