Shari’ar Zaben Kano: Babu wata tattaunawa tsakanin Tinubu da NNPP —APC
APC ta musanta kulla yarjejeniya da Gwamna Abba na Kano ko kuma NNPP don yin sulhu kan hukuncin kotun koli a shari’ar zaben gwamnan jihar.
Jam’iyyar APC ta musanta batun kulla yarjejeniya da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ko NNPP kan hukuncin da kotun koli za ta yanke kaza gwamnan jihar.
Kotun sauraren kararrakin zabe da ta daukaka kara dai sun tsige Gwamna Abba tare da ayyana dan takarar APC, Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris — amma Abba ya daukaka kara hukuncin zuwa kotun koli.
- Buhari @81: Abubuwa 10 da ba za a manta ba
- Musulma ta raba wa marayu da zawarawa Kirista kayan Kirsimeti a Kaduna
APC ta karyata ikirarin cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya baki a lamarin don ganin Abba ya ci gaba da zama gwamna sannan daga bisani ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC.
A wata sanarwa da shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas ya fitar, ya ce baba kamshin gaskiya a maganar sulhu tsakanin NNPP da APC domin sauya hukuncin kotun koli.
Ya ce, “jita-jita ake bazawa cewa NNPP ta tattauna da shugaban Tinubu kan ya sa baki a lamarin domin dan takarar jam’iyyar NNPP ya ci gaba da zama gwamnan Kana sannan ya koma APC.
“Babu inda shugaban kasa ko wani shugaban jam’iyya ya yi irin wannan taro. Shugaban Tinubu bin dimokuradiyya ne da kuma dokar kasa don haka ba zai yi haka da mutanen da suka saci kuri’u ko suka karya dokar zabe ba.”
A baya-bayan nan dai an dinga yada cewa APC da NNPP suna duba yiwuwar yin sulhu kan batun shari’ar zaben gwamnan Kano.
Duk da haka dai ana jiran tsammanin ranar da kotun koli za ta sanya domin yanke hukunci kan.