Babu Hannun Fulani a Kisan Budurwar Da Aka tsinci Gawarta – Gwamnatin Ebonyi
Kwamishiman Yada Labarai na Jihar, Uchenna Orji, ya ce ko a kusa da wurin da lamarin ya auku babu makiyaya.
Gwamnatin Jihar Ebonyi ta ce rade-radin da ya janyo muhawara mai zafi a kafafen sada zumunta cewa Fulani ne suka kashe wata budurwar da aka tsinci gawarta a dajin jihar ba gaskiya ba ne.
Kwamishiman Yada Labarai na Jihar, Uchenna Orji, ya bayyana cewa ko a kusa da wurin da lamarin ya auku babu makiyaya.
- Talauci Ne Musabbabin Tabarbarewar Tsaro —Zulum
- Za mu binciki malamin da ya daki dalibarsa da gora —Gwamnatin Kaduna
Budurwar mai shekaru 17 da bayanai ke nuna ’yar kauyen Onicha Igboeze ce, an kashe ta ne a kan hanyarta ta komawa kauyensu daga Agbabor-isu.
To sai dai wasu mazauna jihar sun yi ta yada cewa Fulani makiyaya ne suka kashe ta, har abin ke neman tada kura a kafafen sada zumunta.
Kwamishinan ya ce, “Duk da cewa gwamnati na Allah wadai da kisan, amma tana tabbatar wa al’umma cewa rade-radin shifcin gizo ne kawai, domin har yanzu ba mu gano wadanda suka aikata ta’asar ba.
“Sai dai da alama wanda ya kashe ta ya bari sai da take hanyar dawowa daga aikin sarrafa rogo tukun, a yadda aka samu gawar”, in ji Kwamishinan.
“Muna fatan kowa zai kwantar da hankalinsa domin bai wa gwannati dama, ta zakulo wadanda suka yi wannan aika-aikar”.