Bacewar Janar Alkali: Sojoji sun kama mutane 13 da ake zargi

Rundunar sojojin Najeriya ta kama mutane 13 wadanda ake zarginsu da hannu a bacewar Manjo Janar Idris Alkali wadanda suka tura motarsa cikin kududdufin Dura-Du a karamar hukumar Jos ta kudu dake jihar Filato ranar 29 ga Satumba 2018. A cikin wadanda aka kama akwai matar da ta hada kai da mata sama da 500 […]

Bacewar Janar Alkali: Sojoji sun kama mutane 13 da ake zargi

Rundunar sojojin Najeriya ta kama mutane 13 wadanda ake zarginsu da hannu a bacewar Manjo Janar Idris Alkali wadanda suka tura motarsa cikin kududdufin Dura-Du a karamar hukumar Jos ta kudu dake jihar Filato ranar 29 ga Satumba 2018.

A cikin wadanda aka kama akwai matar da ta hada kai da mata sama da 500 don gudanar da gangamin tsirara a ranar 22 ga Satumba don nuna rashin amincewar su da sojoji su yi binciken kududdufin da ake zargin ana batar da mutane a ciki.