Rancen karo aure ya ta da hargitsi a Iraki

Bayar da bashi ga magidanta masu neman karo aure na neman kawo yamutsi tsakanin ma’aurata a kasar Iraki. Bankin Al-Rasheed na kasar ya fitar da tsarin bayar da rancen Dinare milyan (10), kimanin Dalar Amurka ($8,378) ga duk mijin da ke da son yi wa matarsa kishiya, wanda hakan ya jawo mata da dama a […]

Rancen karo aure ya ta da hargitsi a Iraki

Bayar da bashi ga magidanta masu neman karo aure na neman kawo yamutsi tsakanin ma’aurata a kasar Iraki.

Bankin Al-Rasheed na kasar ya fitar da tsarin bayar da rancen Dinare milyan (10), kimanin Dalar Amurka ($8,378) ga duk mijin da ke da son yi wa matarsa kishiya, wanda hakan ya jawo mata da dama a kasar yin bore.

“Bayar da bashi ga ma’aikata da bankin Al-Rasheed ke yi abun kunya kuma allawadai ne.

“Dalilin da bankin gwamnatin da ake gani da kima ya bayar na ba ma’aikatansa rance su yi wa matansu kishiya shi ne ma abin da ya fi ban kunya”, inji ‘yar siyasa a kasar Iraki, Hanan Al-Fatlawi.

Ta ce matakin da bankin ya dauka kaskantar da mata ne, inda ta ke cewa “mata ba kayan sayarwa ba ne”.

Rizan Sheikh Dlei, ‘yar Majalisar Dokokin Iraki, ta bukaci Firaminista Mustafa Al-Kadhimi da ya ba da umarnin soke rancen karo auren wanda ta ce na iya sa mata yin zanga-zanga.

Al-Fatlawi ta kara da cewa ya kamata gwamnatin kasar ta fito da sabbin tsare-tsaren da za su ba wa bankuna damar daukar mata aiki domin samun abin da za su dogara da kansu.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7