Badakalar Abdulrasheed Maina ta dauki sabon salo
A ranar Larabar da ta gaba ne iyalan tsohon Shugaban Kwamitin Shugaban kasa na Garambawul ga Tsarin Fansho, Abdulrasheed Maina suka bayyana cewa gwamnatin Buhari ce ta nemi taimakon maigidan nasu don taimaka mata wajen daidaita harkokin fanshon kasa, amma aka yi masa sakayya da wannan jafa’i. Mai magana da yawun iyalan Maina, Malam Aliyu […]

A ranar Larabar da ta gaba ne iyalan tsohon Shugaban Kwamitin Shugaban kasa na Garambawul ga Tsarin Fansho, Abdulrasheed Maina suka bayyana cewa gwamnatin Buhari ce ta nemi taimakon maigidan nasu don taimaka mata wajen daidaita harkokin fanshon kasa, amma aka yi masa sakayya da wannan jafa’i.
Mai magana da yawun iyalan Maina, Malam Aliyu Maina ne ya bayyana haka ga manema labarai a Kaduna, sannan yay i alkawarin cewa za su tona asirin wadanda ke hana ruwa gudu a fadar shugaban kasa. “Mu na masu shelantawa duniya cewa, dan mu ba barawo ba ne, shi maceci ne ma ga kasar nan wanda ya kawo gyara a harkar fanshon kasar nan, wanda kokarinsa da jajircewarsa ne ya kawo karshen watangariyar dubban ‘yan fansho a titunan kasar nan baki daya.”
“Abu ne sananne cewa Abdulrasheed Maina ya inganta harkokin fanshon kasar nan, in da ya dakatar da satar da ake ga asusun fashon a kullu yomin da suka hada da Hukumar Fansho ta kasa da kuma Fanshon ‘Yan Sanda da sauransu. Irin wannan sadaukarwa ce ta ja hankalin wannan gwamnati ta nemi taimakonsa wajen tsamo kasar daga badakalar fansho,” in ji shi.
Ya kuma kara da cewa, “Amma mu iyalansa mun fahimci cewa akwai ‘yan hana ruwa guda daga fadar shugaban kasa wadanda ke amfanin da wata dama don tozarta Maina da iyalansa baki daya. Sun ma kai yin amfani da EFCC wajen likawa gidajenmu jan fanti, cewa ana bincike akansu. To yana da kyau EFCC ta sani cewa Maina ya gaji dukiya mai tarin yawa daga mahaifinsa a Kaduna da Abuja wadanda aka gina su tun kafin an haife shi. Koda yake muna sane cewa wannan yunkuri ba kawai son tadiye Maina ba ce, har ma da kokarin bata sunan Gwamnatin Muhammadu Buhari, da Ministan Shari’a, Abubakar Malami. Amma a halin yanzu muna shirin daukar matakan shari’a akan batun,” a cewar iyalan.
Koda yake tuni Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umarnin korar AbdulRasheed Maina a wani sakon da aka wallafa a shafinsa na Twitter, Shugaba Buhari ya ce a kori Abdulrasheed Maina daga aiki nan take, a kuma yi bincike game da yadda aka yi ya koma aikin gwamnati.
Kazalika, shugaban kasar ya umurci shugabar ma’aikatan gwamantin tarayyar Oyo-Ita Winifred Ekanem, ta mika rahoton binciken ga ofishin shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, Abba Kyari, kafin a tashi daga aiki ranar Litinin, kuma ta mika rahoton kamar byadda aka bukata.
A baya bayan nan dai masu fafutuka sun bukaci Shugaban Muhammadu Buhari ya kama tsohon shugaban kwamitin yin garambawul ga tsarin fanshon, Abdulrasheed Maina, in har da gaske yake yaki da cin hanci da rashawa.
Haka kuma shugaban kwamitin da ke bai wa Shugaba Buhari shawara kan yaki da cin hanci da rashawa, Farfesa Itse Sagay, yana sahun gaban cikin masu kiran da a kama tare da hukunta shi.
Farfesa Sagay ya ce ya kamata a hukunta duk wanda yake da hannu a mayar da Abdulrasheed Maina bakin aiki domin su ma sun taimaka wajen aikata laifi. Baya ga Farfesa Itsey Sagay, fitaccen lauyan nan, Femi Falana, shi ma ya fito ya ce dole a kama Abdulrasheed Maina domin ya amsa tuhume-tuhumen da hukumar EFCC take masa.
Ya kuma ce ya zama wajibi a hukunta dukkan masu hannu a mayar da Maina aiki domin suna neman su hana ruwa gudu ne a yakin da shugaban kasar ke yi da cin hanci da rashawa. Bugu da kari ita dai hukumar EFCC ta garkame wasu gidajen Abdulrasheed Maina a Abuja da kuma Kaduna, sannan ta ayyana shi ruwa-a-jallo don fuskantar bincike kan zargin da ake ma sa.
Kawo yanzu dai fadar shugaban kasar ba ta ce komai game da rahotan maida Abdulrasheed Maina bakin aiki wanda shugabar ma’aikata ta kasa ta aike kamar yadda aka bukace ta. Sannan sanarwar da iyalan nasa suka fitar ya kara sanya dambarwar cikin duhu game da makomar Maina. Koda yake lokaci ne kawai zai fayyace irin matakin da Shugaban Buharin zai dauka game da lamarin, inda wasu ke ganin Ministan Shari’a da Ministan Harkokin Cikin Gida da Shugabar Ma’aikatan Najeriya za su iya fuskantar matsala bisa dawo da Maina a bakin aiki, tun bayan da Hukumar EFCC ta ayyana shi cikin wadanda ta k enema ruwa a jallo bisa bacewar kudin fansho fiye da naira biliyan 100.