Badakalar da Charles ya yi kafin zamansa Sarkin Ingila
Charles ya kasance saraki mai yawan janyo ce-ce-ku-ce a tsawon lokaci.
Charles, sabon Sarkin Ingila, ya kasance saraki mai yawan janyo ce-ce-ku-ce a tsawon lokaci.
Ce-ce-ku-cen sun danganci alakarsa da budurwarsa, a lokacin da yake auren Gimbiya Diana da zargin katsalandan a harkokin siyasa da wasu abubuwan kunya da suka shafi hadimansa.
- Muhimman alkaluma kan rayuwar Sarki Charles III
- Dalilin da Shugaban Rasha ba zai halarci jana’izar Sarauniyar Ingila ba
Babban dan san Sarauniya Elizabeth II, ba shi da farin kamar mahaifiyarsa, wanda hakan karin kalubale ne ga sabon sarki.
Da cikin rikinsa ya tsinci kansa a ciki har da na zargin rashin kulawa da matarsa ta farko, Gimbiya Diana.
Duk da cewa a baya-bayan nan ya samu yabo a kafofin yada labarai, jaridu na yawan sukar sa kan yin nesa-nesa da jama’a.
Fim din matsalolin aure da ya fuskanta, ‘The Crown’ mai dogon zango a Netflix ya sa wasu tauyasa masa, shekaru da dama bayan faruwar abin.
Ya kuma fuskanci zarge-zargen yin katsalandan a harkokin siyasa da suka shafi gine-gine, kiwon lafiya da sauyin yanayi.
A 2021, dambarwa ta sa hadiminsa da ya fi aminta da shi yin murabus a karo na biyu a aikinsa na gidan sarauta.
Da yake tsokaci a 2021 kan kan badakalar karbar kudi don karrama wani Balarabe, da ta shafi kungiyar jinkai ta Charles, marubucin sarauta Penny Junor ya ce, “Ina ganin wadannan abubuwan za su kawo mishi matsala, daga ‘Saurutar’ zuwa sauran abubuwa na zahiri a rayuwa da sauransu.
“Wadannan abubuwa ne masara dadi. An fi son sarauniya a kan Charles.
“Ina ganin ko ma mene ne, sai ya yi da gaske, amma babu yadda za a yi wadannan abubuwan da aka bankado su taimaka masa.”
Cin amanar aure
Martabar Charles ta samu matsala sosai a lokacin rabuwarsa da Diana, wanda ke cike da rudani.
A wata hira ta musamman da aka yi da ita a 1995, inda ta bayyana damuwarta kan alakarsa da budurwarsa Camilla Parker Bowles, Diana ta ce, “mutum uku” ne a cikin aurenta.
A 1992 ma’auratan suka sanarwa mai ban mamaki cewa za su rabu.
Bayan sabanin da suka samu a tattauna da shirin ‘Panorama’ na kafar BBC ya yi da su, daga karshe suka amince su rabu.
Da take ba da nata bahasin abin da ya faru – tare da ikirarin cewa ta ci amanar aure – Diana ta bayyana irin wahalar da ta sha a wurin dangin gidan sarautar.
Ta kuma soke su tare da diga ayar tambaya kan dacewar Charles da zama Sarkin Ingila.
Bayanan nata sun tayar da kura, amma kuma sun jawo mata farin jini, musamman bayan rasuwarta a wani hatsarin mota a 1997 a birnin Paris na kasar Faransa.
An dauki lokaci ana sukar Charles kan zama silar cin amanar auren da ya yi sanadiyyar rabuwarsu.
Kazalika an zargi gidan sarautar da yin watsi da rasuwarta, wanda ake ganin ya saba wa dabi’a.
Daga baya a hankali ya samu goyon bayan jama’a da kuma yarda da cewa ya sami farin ciki tare da Camilla, wacce ya aura a 2005.
Badakalar Black spider
Charles ya tayar da kukra bayan ya fito bainar jama’a ya yi magana tare da matsin lamba a sirrance ga daidaikun ’yan siyasa kan sha’anin kiwon lafiya mai cike da rudani a Birtaniya.
A wasu jerin wasiku tsakaninsa da wasu ministoci da aka bankado kuma baya-bayan nan suka yi tashe, an ga yadda yake yi musu tambayoyi kan wasu batutuwa.
A 2015 ne aka fitar da wasikun, wadanda suka shahara da sunan “Black Spider” saboda yanayin rubutunsa.
An fitar da wasikun ne a sakamakon shari’ar da aka yi sama da shekara 10 ana tafkawa da jaridar The Guardian.
Wasikun sun hada da wani a kan halin da wani kifi nau’in Patagonian Toothfish da shirin gine-gine da ya haifar da ce-ce-ku-ce.
Sukar da ya yi kan tsarin gine-ginen alfarma ya fara daukar hankali ne a 1984, lokacin da ya ce sauya fasalin Gidan Adana Tarihi na Kasa da ke London daidai yake da “sanya gyambo a fuskar amini mai kyan fuska.”
Bayyanar abin da kunshe a wasikun ‘Black Spider’ ta haifar wa yarima mai jiran gado a lokacin matsala da zargin sa da wuce iyaka.
Amma a wata hira da aka yi da shi a bikin cikarsa shekara 70 a 2018, Charles ya ce bai taba shiga harkar siyasar jam’iyya ba kai-tsaye, saboda ya fahimci san matsayinsa na Yariman Wales kuma basarake.
Badakalar karbar rashawa
A baya-bayan nan wata dambarwa ta kunnno kai kan badakalar kabar na goro domin bayar da lambar yabo.
Jaridu sun bankado yadda hadimansa mafiya kusa da shi suka shirya bayar da lambar yabo da takardar shaidar zama dan kasar Birtaniya ga wani Balarabe, dan kasar Saudiyya, wanda ya bayar da makudaen kudaden ga wasu ayyukan tallafi da ke da alaka da Charles.
A 2021, tsohon dogarinsa da ya samu karin girma har ya zama babban jami’in gidauniyarsa ta agaji, Michael Fawcett, ya yi murabus bayan an fara bincike na cikin gida kan zargin.
Wannan dai shi ne zargi na karshe da aka yi wa Fawcett – da kuma ubangidansa, Charles.
A 2003 Fawcett ya sauka daga mukaminsa bayan an zarge shi da saba dokokin fadar Ingila da kuma karbar alfarmar sarauta.
Daga bisani dai an wanke shi daga zarge-zargen rashawa a kan sayar da kyaututtukan sarauta da ba a so, amma wani rahoto na cikin gida ya samu wasu daga cikin dangin Charles da laifin “mummunar gazawa”.