Badakalar cinikin sabuwar Makabartar Hausawan Agege
Tsohuwar makabatar Hausawan Agege ce makabartar da ilahirin ‘yan Arewa mazauna Legas ke tinkaho da ita, domin ana kawo mamata daga sassa daban-daban irin su Idiarba, Apapa cikin garin Legas dama wadansu sassan jahar Ogun. Sama da shekaru goma da suka shude mutanen garin Agege suka ga ya dace su samar da sabuwar makabarta kasancewar tsohuwar ta cika […]
Tsohuwar makabatar Hausawan Agege ce makabartar da ilahirin ‘yan Arewa mazauna Legas ke tinkaho da ita, domin ana kawo mamata daga sassa daban-daban irin su Idiarba, Apapa cikin garin Legas dama wadansu sassan jahar Ogun.
Sama da shekaru goma da suka shude mutanen garin Agege suka ga ya dace su samar da sabuwar makabarta kasancewar tsohuwar ta cika domin duk sanda za ayi sabon kabari sai an tono kasusuwa. Haka ya sa suka kafa gidauniyar ‘Fauzan Azim’ wacce ke da alhakin tara kudade da sayan sabuwar makabarta.
Mutanen ciki da wajen Agege sun bada gagarumar gudunmawa. Fauzan Azim ta yi ta bibiyan mutane ciki da wajen Jahar a gidajensu da kasuwaninsu, a wajen tarukan jama’a, mai taro da kwabo, ta yadda aka hada kai ba tare da banbance-babancen akida ba aka tara makudan kudade. Sai dai kash! har yanzu bayan sama da shekara goma hakar ba ta tarar da ruwa ba.
Duba da yadda matsalar da ake fuskanta a tsohuwar makabartar na ta ci gaba, sai wadansu matasan Agegen suka yi yunkurin magance matsalar, inda suka kafa kungiyar matasa domin su bada gudunmawarsu wajan samar da sabuwar makabarta.
Shugaban kungiyar Alhaji Auwal Sani, wanda aka fi Sani da Alfa Auwalu, ya fada wa Aminiya dalilansu na kafa kungiyar, “Na farko ni ba dan Fauzul Azim ba ne, dalilin yunkurinmu shi ne wata baiwar Allah ta rasu kusan shekara guda kenan da mukaje binne ta sai muka ga an hako mutum sukutum daga kabari ganin haka hankalinmu ya tashi nace da wani abokina Idris in har muka mutu bamu magance wanan bala’in ba Allah sai ya tambayemu, sai yace abin da za muyi muje fada.”
“Bayan kwana daya muka kira taron matasa inda muka tara mutum fiye da 50, sai akace to a fitar da jagororin kungiya muka ce ba mukamaine a Gaban mu ba, daga karshe bisa la’akari da tanajin addinin musulunci sai muka yarda da haka inda a ka bani shugabancin kungiyar.
Nan take suka rubuta takarda zuwa fada suka basu lokaci. “Muka fada musu wannan al’amari na makabarta ya ishemu muna neman bayani a kan samar da sabuwar makabarta? Kuma menene mafita? Nan da nan sarkin Agege yaji dadi ya fada mana suma matsalar ta dade tana cimusu tuwo a kwarya saidai Allah bai basu ikon fitowa da maganarba.
“Fauzan Aziz ta sayi sabuwar makabartar ne a shekarar 2015 aka katange wurin saidai ba a fara komi a ciki ba. Sarkin ya umarci Dan iyan Agege Alh Yakubu yai mana jawabi. Kasan cewar Dan Iyan mamba a Fauzan Azim. Shima ya nuna farin cikin sa, ya fada mana a halin da ake ciki masarautar Agege ta yiwa sabuwar makabartar takardun neman izinin gwamnatin Legas na fara binne matattu a wajan. Bayan ya kare bayanansa sai magajin gari Alh Ali zango shima ya yace sunyi kokarin yin aiki a wurin domin a fara binne mamata.”
Kasancewar wajan wurin ajiyyar sharar karafa ne ada. Injiniyansu yace kasar wajan ta mutu sai an kwasheta a zuba sabuwa kuma wurin zai ci akalla tifa 300 kuma alokacin ana sayar da duk tifar kasa daya naira 30,000, sai muka ce lallai aiki ya sami matasa, Daganan Sardaunan Agege Alh Sani Sha’aibu yace kamata yayi muje mu sami shuwagabannin Fauzan Azim don sune suka sayi sabuwar makabartar.
Bamuyi kasa a gwiwa ba muka garzaya muka sami shugaban Fauzan aziz Alhaji dan liti Dakta. Muka sanar da shi dalilan zuwan mu. Ya nuna mana check-check din da suka biya yace a wurin wasu matasan Hausawa suka sayi filayen bayan sunsaya daga iyalan gidan Olalabi, matasan sunyi yunkurin gina wajan hukuma ta hanasu bisa dalilan rashin cika wasu ka’idoji a cewarsa.
Daga nan ne kugiyar matasan ta nufi sabuwar makabartar don ta fara aiki ta toshe wata magudanar ruwa sanan ta rufe wajan da gate, bayan kwana daya da haka sai aka zo aka ce musu wasu sun zo da ‘yan sanda sun buge gate din sun kawo tifar Yashi sun zuba a wajan. “Dama can munada labarin wasu na ikirarin mallakar wajan, hakan da mukayi shi ya bamu ikon tabbatar da haka. Sai muka kira magatakardar Agege Alh Sabo da Shugaban kungiyar Fauzan Azim tare da sakataren ta muka hadu a wajan da sauran mutanen Gari, sai akace ba hayaniya za a yi ba akwai wani mutum mai gida a wurin muka sameshi don bin bahasi, mutumin ya shaida mana cewa Fauzan Azim basu sayi filin bisa ka’ida ba, domin akwai iyalan gidan Arthur da suma ke ikirarin mallakar wajan. Nanfa Fauzan Azim suka ce mu tuntubi lauyansu Olalaikan Yusuf (SAN). Muka je muka same shi ya mana bayanan da ba mu gamsu dasu ba, ya nuna mana takardar filin sai dai ba a nuna mana na ko wani fili daban -daban ba, hakan yasanya shaku a zukatanmu.
Daga nan muka sanar da rundunar ‘yan sanda. Daga bisani suka kiramu tare da iyalan gidan Arthur da na Olalabi, dukannin bangarorin biyu sukazo da takardar plan din su inda aka tura Alausa don tantancewa.
Mun bada kudi naira100,000 ga iyalan gidan Olalabi don shigarda takardun, mun kuma kashe kudade daban-daban ganin haka mukace ba zamu kuma kashe kudinmu ba a binciken filin da bamu muka saya ba. Domin shiga rigimar filin ba namu bane burun mu filin ya samu mu fara aiki, Fauzan Azim keda alhakin koma nawane a rikicin filin don su suka saya inji” Alfa Auwalu.
Masarautar Agege ta bakin dan Iyan na Agege ta tabbatar wa Aminiya dukkanin bayanan da Alfa Auwalu ya yi, kana dan iyan ya kara da cewa, “Abin da ya ba mu mamaki a lamarin sayan sabuwar makabartar shi ne, ta yaya za a yi lauyan masu sayarwa ya zamo na masu saye? Mun yi tsokaci a kan hakan sai shugabannin Fauzun Azim suka yi amfani da karfin iko da isa suka bai wa lauya Yusuf (SAN) ragamar. gashi abin da muke gudu na so ya faru.”
dan Iyan ya kara da cewa masarautar Agege ta kafa kwamiti da yayo bincike bisa sahihancin cinikin da akayi na sabuwar makabartar inda kwamitin ya gano cewa akwai Lauje a cikin nadi a cikin cinikin, binciken da kwamitin yayi ya gano cewa wani bankin ‘yan kasuwa da ke karkashin bankin Union bank na ikirarin mallakar filin bayaga iyalan gidan Arthur, masarautar ta Agege ta baje wa AMINIYA tarin takardurdun hojjojin da ta tattaro alokacin binciken kwamitin.
Baya ga binciken ne masarautar ta tura wakilai wadanda suka ziyarci lauya Yusuf (SAN) domin su tattauna dashi akan batun. Wakilan basu gamsu da abin da lauyan ya fada masu ba. dan-iyan Agege ya ce a yanzu dai fatan masarautar shi ne yadda za a sami damar mallakar wannan sabon filin makabatar, domin a duk fadin Agege babu fili babba wanda ya dace da yin makabarta kamarsa. Yai kuma kira ga daukacin al’ummar musulmi da su kaiwa mutanen Agege dauki Domin a samun saukin wannan musifa.
Shugaban gidauniyar Fauzan azim Alh Danliti Dakta fadawa Aminiya sun sayi filin sabuwar makabartar akan kudi naira miliyan 15 dadubu 250. Ya ce dalilin da yasa suka baiwa lauya Yusuf (SAN) wuka da nama kuwa shi ne yasan hawa da sauka a sha’anin filin, domin kuwa shi ne ya fara siyawa matasan Agege filin a hannun dangin gidan Olalabi dan haka ta bashi ragamar sayen filin. “A inda yazama lauyan masu saye da masu sayarwa.” Yace kuma lauyan ya basu tabbacin ingancin cinikin sannan yayi alkawarin daukar nauyin duk abinda kaje ya komo. Shugaban ya yi watsi da duk binciken da kwamitin masarautar Agege ya gudanar yace babu wanda ya ja da wakilcin da suka baiwa lauyan.
Duk da wannan takun saka, burin musulmai mazauna Agege shi ne su sami mafita wajen inda za sudinga binne mutane kada ta kai cewa sai an fara binne mutum fiye da daya a kabari guda ko kuma a ce sai an dinga dauko gawa daga kudu zuwa areaway dan binne wa ba.
Jagoran masu tsaron tsohuwar makabartar Alhaji Babangida Haladu,ya ce a yanzu ba su da wata masaniya a kan sabuwar makabarta. “A yanzu dai tsohuwar makabarta muka sani kuma ba abin da za mu yi sai addu’a ga wadanda suka samar da Ita. Na yi shekara 45 ina aiki a nan ba mu da wata makabartar da ta fi wannan, wadanda suka assasata sun mana gata, ko ka san nawa ake binne gawa a Legas? To naira 165,000 ne, amma a nan ba a karbar komai, ka ga ba abun da za mu ce sai godiya. Ba a taba kawo gawa an koma da ita ba. sai dai muna cin karo da kasusuwa in mun zo hakar sabon kabari mukan mayar mu binne bayan mun binne gawar “.