Badakalar Dasuki: Abin da ya sa ba mu gayyaci Jonathan ba – Shugaban EFCC
Mukaddashin Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) Malam Ibrahim Mustafa Magu ya ce bas u gayyaci tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ba ne game da binciken da suke yi kan karkatar da kudin sayo makamai da ya taso daga ofishin Mashawarcinsa kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki saboda takardun da […]
Mukaddashin Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) Malam Ibrahim Mustafa Magu ya ce bas u gayyaci tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ba ne game da binciken da suke yi kan karkatar da kudin sayo makamai da ya taso daga ofishin Mashawarcinsa kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki saboda takardun da suka kunshi rarraba kudin ba su nuna ya amince da a raba su domin kamfe din siyasa ba, abin da ke nuna ba a kashe kudin ba ne kawai kan abin da aka shirya kashe su ba.
Malam Ibrahim Magu ya bayyana haka ne a ranar Litinin lokacin da yake ganawa da kafafen watsa labarai na Intanet a Legas, inda ya ce yanzu aka fara yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan, kuma babu abin da zai hana gurfanar da masu almundahana a gaban shari’a komai girman mutum.
Malam Magu ya ce tsohon dan takarar Gwamnan Jihar Kano a tsohuwar Jam’iyyar CPC kuma daya daga cikin na hannun daman Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Birgediya Janar Lawal Jafaru Isa wanda aka kama a baya-bayan nan kan karbar Naira miliyan 170 daga Sambo Dasuki ya dawo da Naira miliyan 100 daga ciki kuma ya dauki alkawari a rubuce zai dawo da sauran nan da lokaci kadan. Kuma duk da ya dawo da kudin za a gabatar da shi a gaban shari’a don hukunta shi.
Malam Ibrahim Magu ya kuma ce Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar PDP ta kasa Mista Olisa Metuh, ya shaida wa hukumar EFCC cewa zai gwammace ya shiga yajin cin abinci da ya dawo da kudin da ya karba daga Dasuki.
Ya kuma ce an sake kama tsohon Shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa na Najeriya (NIMASA) Mista Patrick Akpobolokemi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ne saboda an samu sababbin hujjoji kan zarginsa da almubazzaranci da Naira miliyan 34 da rabi da kuma wata Naira miliyan 600 a lokacin da yake shugabancin hukumar.
Ya ce ya karya belin da aka ba shi lamarin da ya sa aka kama lauyan da ya karbi belinsa a wajen kotu a Legas, bayan da ya ki bin umarninsu nay a koma zuwa ofishin EFCC tare da su.
Magu ya nuna takaici kan yadda wasu mutane ke nuna cewa ana zabe wajen yaki da cin hancin, inda ya ce babu wanda ke tsoma wa Hukumar EFCC baki a yaki da cin hanci da rashawar da take yi.
Ya ce Hukumar EFCC ana jan kafa ne a shari’un EFCC saboda da dama daga cikin ’yan siyasa idan mutum ya saci Naira biliyan 10, sai ya ajiye Naira biliyan biyar don jirar ko za a gurfanar da shi a gaban kotu. “Sai ya dauki manyan lauyoyin Najeriya, sannan alkalai su rika zarginmu da cewa ba mu yi cikakken bincike ba domin a lalata shari’ar,” inji shi.
Ya ce yaki da cin hanci da rashawa yaki ne na kowa da kowa don haka ya shawarci kafafen watsa labarai su hada hannu da Hukumar EFCC wajen wannan yaki wanda nasararsa za ta amfani ’yan baya.