Badakalar Dasuki: An gano Naira biliyan daya da rabi a asusun dan tsohon Minista
Wani dan canji ya shaida wa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) cewa an tura wa asusunsa Naira biliyan daya da rabi domin ba dan wani tsohon Ministan Kudi.Jaridar The Nation da ta ruwaito rahoton ta ce Salisu Umaru ya ce bai san me dan tsohon Ministan ya yi da kudin ba. […]
Wani dan canji ya shaida wa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) cewa an tura wa asusunsa Naira biliyan daya da rabi domin ba dan wani tsohon Ministan Kudi.
Jaridar The Nation da ta ruwaito rahoton ta ce Salisu Umaru ya ce bai san me dan tsohon Ministan ya yi da kudin ba. Ba a bayyana sunan tsohon Ministan da dansa ba, “domin kada a samu matsala a binciken da ake yi.” Kuma ana da yakinin kudin wani bangare ne na Dala biliyan daya da miliyan 100 na sayo makamai da aka karkatar.
Har wa yau a karshen mako Rundunar Sojin Najeriya ta maye wani jami’inta da ake bincika kan badakalar sayo makaman wato Kanar Nicholas Ashinze da Kanar M.A. Abdullahi a matsayin jami’in soji na ofishin Jadancin Najeriya da ke Jamus.
Salisu, wanda ya yi wa EFCC bayanin dalla-dallar yadda Naira biliyan daya da rabin ta shiga asusun kamfaninsa, ya ce bai san kudin da suka fito daga ofishin Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro na mene ne ba.
Ya ce: “Hukumar EFCC ta gayyace ni kuma lokacin da na kai kain an nuna min bayanin asusun kamfanina na Jabama Ada Global Nigeria Limited da ke bankin Zenith Bank, inda aka turo Naira miliyan 500 a ranar 5/2/2015 da kuma Naira biliyan daya a ranar 16/4/2015 zuwa asusun daga ofishin Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro. Game da turo Naira miliyan 500 zuwa asusun kamfaninsa a ranar 5/2/2015, ina mai bayyana cewa: A waccan rana (5/2/2015) na biyan kwatankwacin Dala dubu 380 da 952 ga dan tsohon Ministan, wato daidai da Naira miliyan 500 din kan Naira 210 ga kowace Dala. Ban san kudin na mene ne ba. Ni kasuwancin saya da sayar da daloli nake yi. Don haka dan Ministan ne kawai zai iya bayanin kudin na mene ne. dan Ministan ya sanya hannu ya karbi wannan Naira miliyan 500.”
“Game da Naira biliyan daya da aka tura asusun kamfanina a ranar 16/4/2015, ina bayyana cewa an rarraba kudin kamar haka: Dala miliyan daya, daidai da Naira miliyan 220 da Dala dubu 327 (daidai da Naira miliyan 72 da dubu 600) an bayar da tsabar kudinsu ga dan Ministan, yayin da Naira miliyan 704 da dubu 400 aka tura asusun ajiya daban-daban bisa umarnin dan Ministan. Ya bayar da wasu umarnin ne ta hanyar sakon waya. Wasu umarnin daga babansa aka karba. Kuma ina bayyana cewa ban san Naira biliyan dayar ta mece ce ko me za a yi da ita ba.”
Zaben farko na Kanar M.A. Abdullahi don yin aikin ya hadu da kin amincewar tsohon Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya Laftana Janar Kenneth Minimah.
An ce Janar Minimah ya fi son Kanar Ashinze saboda yana jin harshen Jamus sosai. Kuma Rundunar Sojin Najeroya ta nemi Kanar Ashinze ya dawo da Naira miliyan bakwai da dubu 300 da aka biya shi da sukahada da kudin alawus na Naira miliyan shida da kudin jirgi Naira miliyan daya da dubu 300.
Jami’in sojan wanda na hannun damar Kanar Sambo Dasuki ne ya bukaci Rundunar Sojin Najeriya ta sanya Hukumar EFCC ta dage takunkumin da ta sanya kan asusuna jiyar bankinsa domin ya samu damar dawo da kudin.