Badakalar kudin makamai: APC ta bukaci Jonathan ya yi bayani kan hannun Asari Dokubo
Jam’iyyar All Progressibes Congress (APC) ta bukaci Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya yi wa ’yan Najeriya bayani kan abin da Mujaheed Asari Dokubo yake yi a cikin jirgin da aka kama da Dala miliyan 9.3 a kasar Afirka ta Kudu, inda aka kama Asari Dokubo da wani dan Najeriya da dan Isra’ila kamar yadda […]
Jam’iyyar All Progressibes Congress (APC) ta bukaci Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya yi wa ’yan Najeriya bayani kan abin da Mujaheed Asari Dokubo yake yi a cikin jirgin da aka kama da Dala miliyan 9.3 a kasar Afirka ta Kudu, inda aka kama Asari Dokubo da wani dan Najeriya da dan Isra’ila kamar yadda wani rahoto da aka buga ya bayyana.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar APC Alhaji Lai Mohammed ya raba wa manema labarai a Abuja a shekaranjiya Laraba, jam’iyyar ta ce tunda Gwamnatin Tarayya ta ce kudin nata ne da aka fitar ta ofishin Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro don sayo makamai, ke nan gwamnatin ta san dalilin hannun dukkan wadanda suke cikin jirgin.
APC ta ce, akwai dimbin tambayoyin da ya wajaba Gwamnatin Tarayya ta amsa kan badakalar ciki har da ko Asari Dokubo dan kwangila ne ko shine mai amfani da makaman, yana sayo makaman ne ma wa kuma da wane dalili.
Jam’iyyar ta ce yin tambayoyin ya zama dole, saboda hatta Mashawarcin Shugaban kasar wanda ya fitar yarjejeniyar sayo makaman don amfani da su, ba shi da iko kuma ba zai iya sayo makamai ga daya daga cikin bangarorin soja ba. Manyan hafsoshin soja suna da kasafinsu daban da na Mashawarcin Shugaban kasa kan Tsaro don sayo makamai.
Jam’iyyar APC ta ce “A karkashin Tsarin Mulki Mashawarcin Shugaban kasa kan Tsaro, mai bayar da shawara ne ba ya da ikon tura sojoji daga kowane bangare su sayo makamai ga kansu. Wadannan makamai da ake cewa za a sayo daga Afirka ta Kudu an yi odarsu ne daga ofishin Mashawarcin Shugaban kasa kan Tsaro, ba wani abu ba ne face, tsabagen karya, kuma hakan ya haifar da shakku kan manufar sayo makaman. Don haka ’yan Najeriya suna son sanin a madadin wa Asari Dokubo yake sayo makaman. Wannan yana da matukar muhimmanci, saboda Dokubo ya rika barazanar ba za a zauna lafiya a Najeriya idan ba a sake zaben mai gidansa Shugaba Jonathan ba. Don haka ’yan Najeriya za su so sanin ko ya fara tara makamai ne domin aiwatar da barazanarsa, tunda nan da ‘yan watanni za a gudanar da zabe.”
Jam’iyyar APC ta kara da cewa: “Idan wadannan makamai na yaki da masu daukar makamai ne kamar yadda gwamnati ta yi da’awa, to me ya hada Dakubo da harkar sayo makamai ga sojojin Najeriya, idan dai da gaske na sojojin ne? Shin gwamnati ba ta tunanin cewa wannan mutum wanda ya taba daukar makami yana yakar kasar nan, ba zai sake daukar makami ya sakr yakar kasar ba? Wace kasa ce za ta lamunce wa wanda ya taba daukar makami yana yakarta ya dawo yana sayo mata makamai? Idan ma gaskiya ne yana sayo makaman ne ga kasar nan, me zai hana ya yi amfani da wannan dama ya cimma mugun nufinsa? Anya ba wannan ne ya sa Asari Dokubo yake fitowa fili gaba-gadi yana maganganun da ya ga dama ba tare da jami’an gwamnati na ja masa kunne ba, yana cewa tilas a sake zaben Shugaba Jonathan ko Najeriya tayi ban kwana da zaman lafiya?”
Jam’iyyar APC ta ce a sanarwarta ta ranar Talata ta bukaci Shugaba Jonathan ya fito ya wanke kansa kan badakalar Dala miliyan 9.3 da Dala miliyan 5.7 da aka kama da suna sayo makaman kuma ya bayyana wa ’yan Najeriya su wane ne ’yan Najeriya biyu da suke cikin jirgin da ya fita da kudi ta haramtacciyar hanya zuwa Afirka ta Kudu. “Yanzu da ’yan Najeriya suka sani mutanen Shugaban kasa ne, labarin ya dauki sabon salo,” inji ta.
Sai ta bukaci Majalisar Dokoki ta kasa ta dauki batun kudin sayo makaman da muhimmanci maimakon watsi da bincike kansa da sunan wasu ka’idojin na Majalisar Tarayya.
Jam’iyyar ta yaba wa kafafen watsa labarai kan yadda suak rika bin diddigin labarin tare da aiki bilhakki domin bankado ’yan Najeriyar da suke cikin jirgin. Ta bukaci kafafen watsa labarai su ci gaba da kasancewa idanu da kunnuwan jama’a tare da fallasa badakalar da ta shafi batun wadda ta yi matukar zubar da mutuncin Najeriya a idon duniya kuma ke iya barazana ga hadin kan kasa.