Badakalar Maina: Shugabannin ma’aikata sun yi cacar baki a fadar Shugaban kasa

Badakalar dawowar AbdulRasheeed Maina,  tsohon Shugaban hukumar yi wa fansho garambawul ta haifar da cacar baki a fadar Shugaban kasa ta Aso da ke Abuja, inda Shugabar ma’aikata ta kasa Winifred Oyo-Ita da Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa, Abba Kyari suka yi musayar miyau kan takardar bin bahasi da Shugaban kasa ya nema da aka […]

Badakalar Maina: Shugabannin ma’aikata sun yi cacar baki a fadar Shugaban kasa

Badakalar dawowar AbdulRasheeed Maina,  tsohon Shugaban hukumar yi wa fansho garambawul ta haifar da cacar baki a fadar Shugaban kasa ta Aso da ke Abuja, inda Shugabar ma’aikata ta kasa Winifred Oyo-Ita da Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa, Abba Kyari suka yi musayar miyau kan takardar bin bahasi da Shugaban kasa ya nema da aka baza wa duniya.

Rahotanni sun ruwaito Oyo-Ita a takardar bayanan tana cewa Shugaba Muhammmadu Buhari na sane da dawo da Maina kan mukaminsa, kuma ta gargaDe shi a kan hakan.

An dai yi wannan takaddamar ne da karfe 10:30 na safe ranar Larabar wannan makon kafin isowar Shugaba Muhammmadu Buhari wajen kaddamar da sabon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Bosss Mustapha, tare da kaddamar da tambarin bikin tuna wa da ’yan mazan jiya na 2018, Daukacin al’amurran da za a fara gabatarwa kafin taron Majalisar Zartarwa.

WaDannan al’amura dai an yi su ne a gaban Shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki da Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara da Shugaban jam’iyyar APC na kasa Odige-Oyegun da shugabannin rundunonin soja da jami’an hukumomin tsaron kasa, tare da abokai da ’yan uwan sabon Sakataren Gwamnatin Tarayyar.

Da isowar Shugabar ma’aikata Dakin taron sai Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban kasa ya far mata kan yadda aka yi ta baza takardar da ta aika musu.

An dai jiwo Oyo-Ita cikin fushi tana cewa ta kai makura a aikin gwamnati, kuma ita ba zaBenta aka yi ba.

Mataimakin Shugaban kasa da ke zaune kusa da Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa, Abba Kyari nan da nan ya shiga tsakani, inda ya gana da shugabannin ma’aikata biyu na tsawon minti biyar. Kuma sabon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Boss Mustapha da Mai bayar da shawara kan harkokin tsaron kasa Babagana Munguno sun samu nasarar shawo kan takaddamar rikicin kafin isowar Shugaba Buhari.

A nata Bangaren Fadar Shugaban kasa ta bayyana dalilin da ya sa ta yi shiru game da takardar da Shugabar ma’aikata ta aike mata, da aka baza wa duniya, wadda aka ruwaito cewa Winfred Oyo-Ita ta ce Shugaba Buhari na sane da dawo da Shugaban hukumar yi wa tsarin fansho garambawul, AbdulRasheed Maina kan mukaminsa.

Babban mai taimaka wa Shugaban kasa kan harkokin watsa labarai da hulDa da jama’a, Malam Garba Shehu ya ce har yanzu fadar Shugaban kasar ba ta tabbatar da cewa shugabar ma’aikatan ce ta rubuta ta ba.

Malam Garba Shehu ya gana da manema labarai, in da ya ce suna ganin takardar ta bogi ce. Don haka ya jadadda cewa da zarar Oyo-Ita ta tabbatar ita ta rubuta to za su mayar da martani.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa Shugaban kasa bai yi wani abu kan rahoton Oyo-Ita ta gabatar masa  game da badakalar da ta kanainaye dawowar Maina, sai ya ce da zarar ya tabbatar da dalilin zai tuntuBi manema labaran, amma bai yi hakan ba, har zuwa lokacin da aka tattara wannan rahoton.