Badakalar makamai: EFCC ta kama Jafaru Isa *Za ta kama wasu manyan mutane kwanan nan
Hukumar Yaki da yi wka Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta kama wani na hannun daman Shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma tsohon Gwamnan mulkin Soja na Jihar Kaduna Birgediya Janar Lawal Jafaru Isa dangane da zargin yana da hannu a badakalar karkatar da kudin sayo makamai.Lawal Jafaru Isa wanda jigo ne a Jam’iyyar APC shi ne […]
Hukumar Yaki da yi wka Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta kama wani na hannun daman Shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma tsohon Gwamnan mulkin Soja na Jihar Kaduna Birgediya Janar Lawal Jafaru Isa dangane da zargin yana da hannu a badakalar karkatar da kudin sayo makamai.
Lawal Jafaru Isa wanda jigo ne a Jam’iyyar APC shi ne dan takarar Gwamnan Jihar Kano a tsohuwar Jam’iyyar CPC ta Shugaba Buhari a zaben 2011 an ce aboki ne na kut ga tsohon Mashawarcin Shugaban kasa kan Tsaro Kanar Sambo Dasuki.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an kama Jafaru Isa ne a gidansa da ke titin Ajayi Crowther a Asokoro, Abuja da misalin karfe 9:00 na dare a shekaranjiya Laraba.
Jaridar ta ce ta samu bayani an gayyaci Jafaru Isa zuwa ya gurfana a gaban Hukumar EFCC a shekaranjiya Laraba domin wanke kansa kan “wasu kudi daga tsohon Mashawarcin Shugaban kasar.
Masu bincike sun ce Jafaru Isa ya karbi Naira miliyan 100 daga Dasuki.
A cewarta wata majiya ta shaida mata maimakon ya amsa gayyatar, sai ya rubuta wa Hukumar EFCC ta hannun lauyansa yana bukatar a dage ranar bayyanarsa a gabanta saboda rasuwar wani dan uwansa. Sai dai kuma hukumar ba ta gamsu da wannan bayani ba, inda ta yanke shawarar kama shi.
Duk kokarin jaridar na jin ta bakin kakakin Hukumar EFCC, Wilson Ujuwaren a safiyar jiya Alhamis kan lamarin ya ci tura.
Kama Jafaru Isa ya zo ne ’yan awanni bayan da Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu ya ce kwanan nan za su kama wasu manyan ’yan Najeriya da ake zargi da hannu a badakalar makaman lokacin da yake ganawa da kafafen watsa labarai na Intanet a Abuja a shekaranjiya Laraba.
Wata sanarwa da kakakin hukumar, Wilson Uwujaren ya fitar ta ruwaito Magu yana cewa “Wasu manyan ’yan Najeriya na cikin wadanda EFCC ta hasko, kuma nan da makonni kadan za su samu kansu a kotu kuma za a sanar da ’yan Najeriya cikakken bayani kan binciken hukumar.” Ya nanata cewa hukumar ba za ta nuna sani ko sabo ba, wajen gudanar da ayyukanta. Kuma ya ce babu ruwan hukumar da batun siyasa.
A farkon wannan mako ne Hukumar EFCC ta yi awon gaba da Kakakin Jam’iyyar PDP ta kasa Olisa Metuh bisa zarginsa da hannu a badakalar, hukumar tana zarginsa da kan karkatar da Naira biliyan daya da miliyan 400 daga ofishin Dasuki zuwa kamfanin Destra da yake da alaka da shi.
Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa Cif Tony Anenih ma fallasar ta shafe shi, inda aka ce ya karbi Naira miliyan 260 daga cikin kudin.
Sai dai lokacin da yake bayani kan yadda ya sarrafa kudin Cif Anenih ya ce ya bayar da Naira miliyan 63 daga cikin kudin ga Alhaji Tanko Yakasai, wanda shi kuma ya ce kudin ba su kai haka ba, kuma an ba su kudin ne su tara don su zagaya kan sarakuna su roki jama’arsu don a gudanar da zaben 2015 cikin kwanciyar hankali da lumana. Kuma ya ce, ya zaga kan sarakunan da suka hada da Mai alfarma Sarkin Musulmi da Sarkin Kano da na Gwandu da Bauchi da daukacin manyan sarakunan jihohin Arewa 19.
Malam Tanko Yakasai ya ce an ba shi kudin ne hade da jaddawalin yadda zai kashe su wajen zagayen, kuma ya yi hakan. Don haka ba zai bayar da da ko sisin kwabo ba, kuma a shirye yake ya amsa kowace irin gayyata daga kowace hukuma a kan haka.