Badakalar N2.9bn: Kotu ta ba da belin Okorocha kan N500m
An ba da shi beli a ranar da za a tantance shi a matasyin mai neman takarar shugaban kasa
Kotu ta bayar da belin tsohon Gwamnan Jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, a kan Naira miliyan 500 tare da kwace takardar fasfo dinsa.
Babban Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta kuma shardanta wa Okorocha, mai neman takarar shugaban kasa, da ya kawo mutum daya da zai tsaya mishi kuma ya ajiye Naira miliyan 500.
- Me Tinubu ya fada wa kwamitin tantance ’yan takarar APC?
- NAJERIYA A YAU: Yadda Tsawaita Lokacin Kamfe Na Zaben 2023 Zai Shafi ’Yan Najeriya
Daliban firamare sun fara shiga kungiyoyin asiri a Ogun — Gwamna
Babbar kotun ta bayar da belin ne a ranar da Okorocha zai bayyana domin tantancewa a gaban kwamitin tantance masu neman takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Hukumar Yaki da Karya Tattalin Arziki (EFCC) ce ta gurfanar da Okorocha a gaban kotun bisa zargin almundanar Naira biliyan 2.9 a lokacin da yake kan kujerar Gwamnan Jihar Imo.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Inyang Ekwo, ya ce dole ne duk mutumin da zai tsaya wa Okorocha ya kasance mallaki gida a Abuja, sannan ya damka wa kotun takardun mallakar filin.
Mai Shari’a Inyang Ekwo ya bayar da belin ne a ranar Laraba a tare da haramta wa Okorocha fita daga Najeriya ba tare da samun izinin kotu ba.
Kotun ta dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 7 zuwa 11 ga watan Nuwamban 2022, bayan ta ba da belin mutumin da hukumar EFCC take tuhuma tare da Okorocha, Anyim Chinenye.
Kawo yanzu dai babu bayani game da ko ya cika sharudan belin da kotun ta gindaya mishi.
An gurfanar da Okorocha mai wakiltar Imo ta Arewa a Majalisar Dattawa ne tare da Chinenye da kuma Naphtali International Limited da Perfect Finish Multi Projects Limited da kuma Consolid Projects Consulting Limited.
Sauran kamfanonin da ake zargin su ne Pramif International Limited, da kuma Legend World Concepts Limited.