Badakalar sayen makamai: An dage shari’ar karar da aka kai Shugaban kasa

A shekaranjiya Laraba ne Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta fara sauraren karar da wasu malaman Jami’ar Bayero ta Kano su hudu da wadansu mutum biyu suka shigar gabanta inda suke karar Shugaban kasa Goodluck Jonathan da Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya, Fasto Ayo Oritsejafor da Majalisar Wakilai kan badakalar makudan kudin da aka […]

Badakalar sayen makamai: An dage shari’ar karar da aka kai Shugaban kasa
Badakalar sayen makamai: An dage shari’ar karar da aka kai Shugaban kasa

A shekaranjiya Laraba ne Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta fara sauraren karar da wasu malaman Jami’ar Bayero ta Kano su hudu da wadansu mutum biyu suka shigar gabanta inda suke karar Shugaban kasa Goodluck Jonathan da Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya, Fasto Ayo Oritsejafor da Majalisar Wakilai kan badakalar makudan

kudin da aka kama a kasar Afirka ta Kudu da sunan sayen makamai.
A wannan zama masu karar da suka hada da Dokta Sa’idu Ahmad Dukawa da Dokta Salisu Shehu da Isa Ibrahim Garba da Kamilu Hassan Kwakwatawa da kuma Umar Jibrin Gwandu sun nemi kotun da ta dage shari’ar zuwa wani lokaci don su samu isasshen lokacin da za su kara wasu abubuwa a cikin karar tasu tare da ba wasu mutane da ke da sha’awar shiga cikin shari’ar damar yin haka.
Wadanda ake kara ba su halarci zaman kotun a wannan rana ba.
Alkalin Kotun Mai shari’a Fatun Liman ya amince da bukatar masu kara inda ya dage shari’ar zuwa ranar 5 ga Nuwamba.
A cikin takardar karar mai shafuka 25 da malaman jami’ar suka gabatar wa kotun sun bukaci kotun ta sa Shugaba Jonatahan ya yi wa jama’a bayani kan damar da yake da ita ta sayen makamai, wanda hakan yake tamkar keta alfarmar mulkin kasa ne.
Sun kuma nemi Shugaba Jonathan ya fito ya bayyana hujjoji da bayanai mai gamsarwa da suka shafi wannan kudi shin mallakar Gwamnatin Tarayya ce sannan ya bayyana gaskiyar mutum biyun da aka kama da hannu a cikin badakalar wadanda a yanzu haka suke tsare.
Haka kuma sun nemi Shugaba Jonatahan ya yi bayani game da dalilin da ya sa shi yin amfani da jirgin shugaban kungiyar Kiristocin duk da jirage kusan goman da gwamnati ke da su. Haka kuma ya fito fili ya yi bayanin dalilin bin barauniyar hanya wajen sayen makaman. Har ila yau akwai bukatar Shugaba Jonathan ya bayyana dalilin yin amfani da kudi tare da kin yin amfani da hanyar gudanar da cinikayya a zamanance.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi