Badakalar sayo makamai: Zan yi magana a lokacin da ya dace – Jonathan
Tsohon Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya ce ba zai ce uffan kan binciken da ake yi kan sayo makamai a zamanin gwamnatinsa don yaki da Boko Haram ba. Jonathan ya bayyana haka ne a shekaranjiya Laraba a wani taro da kulob din Geneba Press Club ya shirya a kasar Switzerland. Tsohon Shugaban kasar wanda […]
Tsohon Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya ce ba zai ce uffan kan binciken da ake yi kan sayo makamai a zamanin gwamnatinsa don yaki da Boko Haram ba. Jonathan ya bayyana haka ne a shekaranjiya Laraba a wani taro da kulob din Geneba Press Club ya shirya a kasar Switzerland. Tsohon Shugaban kasar wanda yake amsa tambayoyi daga mahalarta taron ya ce: “Zan so yi in magana sosai a kan wannan batu (na sayo makamai), saboda ko a can gida, a duk lokacin da na karanta jaridu mutane da dama kan ce akwai bukatar tsohon Shugaba Jonathan ya yi magana (kan batun sayo makamai na Dala biliyan 2.1). Sai dai a kasarmu akwai dokoki; idan batu yana gaban kotu, mutanen da suke da alaka da batun ba a so su yi magana a kai, don ana daukar hakan yi wa shari’a katsalanda ce. Kuma a matsayina na tsohon Shugaban kasa idan na yi tsokaci a kai na iya jawo matsala ga shari’ar da kotu ke yi da shaidun da ake gabatarwa da sauransu. Don haka ba zan yi magana ba, sai an kammala shari’un, amma tabbas zan yi magana a kai.”
Dokta Jonathan ya kara da cewa: “Ba zan son in yi magana musamman a kan sayo makamai na Dala biliyan 2.1 ba, domin hakan bai dace ba, amma in lokacin da ya dace ya zo zan bayyana abin da ke cikin zuciyata.”
Tun farko a jawabin da ya gabatar a taron Dokta Jonathan ya ce, “Giyar mulki da tunanin abin da zai faru bayan an sauka daga mulkin sukan jarrabawa ga mutumin da yake son jama’arsa da kasarsa.”
Ya kara da cewa, a matsayinsa na Shugaban kasa ya yi aiki tukuru domin ya karfafa gwiwar ’yan Najeriya da wadanda ba ’yan Najeriya su zuba jari a kasar. Jonathan ya ce shi da sauran tsofaffin shugabannin kasar nan za su ci gaba da goya wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya a yakin da yake yi da Boko Haram.