Badaru na fuskantar tsigewa a Jigawa

Hankula na ci gaba da tashi a jihar Jigawa dangane da zargin shirin da majalisar dokokin jihar take yi na tsige gwamnan jihar, Muhammadu Badaru Abubakar. Wata majiya ta bayyana cewa tsigewar na daya daga cikin matakan da majalisar ta dauka na tunkarar gwamnan kan zargin sayar da filayen jihar da ke jihar Legas ba […]

Badaru na fuskantar tsigewa a Jigawa

Hankula na ci gaba da tashi a jihar Jigawa dangane da zargin shirin da majalisar dokokin jihar take yi na tsige gwamnan jihar, Muhammadu Badaru Abubakar.
Wata majiya ta bayyana cewa tsigewar na daya daga cikin matakan da majalisar ta dauka na tunkarar gwamnan kan zargin sayar da filayen jihar da ke jihar Legas ba bisa ka’ida ba.
Makon da ya gabata majlisar dokokin jihar ta kaddamar da bincike kan gwamnan kan abin da suka kira baiwa kananan hukumomin jihar 27 damar sayo kayan kujerun makarantun firamare na yankunansu ba bisa ka’ioda ba.