Badi za a kammala titunan jirgin kasa – Sanata Sahabi

Shugaban Kwamitin Sufurin kasa a Majalisar Dattawa, Sanata Sahabi Ya’u kaura ya ce cikin shekara mai zuwa Gwamantin Tarayya za ta kammala gina titunan jiragen kasa da take yi a fadin kasar nan.Sanata Sahabi ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau a karshen makon jiya, inda ya ce gwamnati […]

Badi za a kammala titunan jirgin kasa – Sanata Sahabi
Badi za a kammala titunan jirgin kasa – Sanata Sahabi

Shugaban Kwamitin Sufurin kasa a Majalisar Dattawa, Sanata Sahabi Ya’u kaura ya ce cikin shekara mai zuwa Gwamantin Tarayya za ta kammala gina titunan jiragen kasa da take yi a fadin kasar nan.
Sanata Sahabi ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau a karshen makon jiya, inda ya ce gwamnati ta dukufa don kammala gyaran tsofaffi da gina sababbin titunan jiragen kasa da
za su hada Kudu da Arewa baki daya a karshen badi.
Sanata Ya’u ce “Sababbin ayyukan sun kai kilomita 800 da suka hada daga Gusau zuwa Talata Mafara zuwa Sakkwato, sai kuma daga kauran Namoda zuwa Shinkafi da Sabon Birni zuwa Sakkwato zuwa Illela da kuma Illela zuwa Gwandu zuwa Birnin Kebbi.
Ya ce farfado da harkar sufurin jirgin kasa ana yi ne don inganta harkar sufuri domin harkar sufuri kashin  bayan ci gaban kasa ce da hatta kasashen da suka ci gaba a duniya sune inganta sufurin jirgin kasa.
Sanatan ya ce kasar nan za ta samar da ci gaban sufurin jiragen kasa, inda ma’aikaci zai tashi daga Kaduna ya tafi Abuja aiki ya dawo.