Bafalasdinen da ya shiga yajin cin abinci ya mutu a gidan kaso a Isra’ila
Isra’ila ta tsare Adnan har sau 12, inda ya shafe kusan shekaru takwas a kurkuku.
Bafalasdine Khader Adnan mai alaka da kungiyar da ke ikirarin jihadi ta Falasdinu ya mutu a wani gidan kaso na Isra’ila bayan yajin kin cin abinci na kwana 87.
Hukumomin gidan yarin na Isra’ila sun ce an dauki Adnan, wanda Tel Aviv ta zarge shi da laifin ta’addanci, zuwa asibiti bayan an gaza farfado da shi, an kuma tabbatar da mutuwarsa da sanyin safiyar Talata.
- An yi gakuwa da ’yar Sauraniyar Kudancin Kaduna
- Wanda ya yi wa ’yar shekara 5 fyade a masallaci ya shiga hannu
Isra’ila ta ce Adnan “ya ki yarda a yi masa gwaje-gwaje na lafiya da karbar magani kuma an same shi a sume a cikin dakinsa na kurkuku” da sanyin safiya.
Lauyan da ke kare Adnan ya zargi Isra’ila da sakaci na duba lafiyarsa.
“Bayan kwana 36 da kama Adnan, mun bukaci a kai shi asibitin farar hula inda za a iya duba lafiyarsa yadda ya kamata.
“Abin takaici, sai aka ki yarda da wannan bukata kuma hukumomin gidan yarin Isra’ila suka yi watsi da bukatar,’’ in ji lauya Jamil Al Khatib.
“Da gangan aka kashe Khader Adnan,” in ji kungiyar fursunoni ta WAED a Gaza a wani martani da ta yi a hirarta da Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters.
Isra’ila ta harba rokoki a Zirin Gaza
Jim kadan bayan sanar da mutuwar Adnan, an yi ta jin karar jiniya daga kan iyakokin Isra’ila da Gaza, lamarin da ya sa mazauna yankin tserewa don samun mafaka.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce an harba rokoki uku daga Zirin Gaza zuwa yankin Isra’ila, amma ba su fada kan jama’a ba.
“Yakinmu yana ci gaba kuma makiya za su gane cewa laifukan da suka aikata ba za su wuce ba tare da an mayar musu da martani ba.
“Za a ci gaba da tsayin daka da dukkan karfin gwiwa da azama,” a cewar kungiyar da ke ikirarin jihadi ta Falasdinu a cikin wata sanarwa.
Adnan, mai shekaru 45 dan asalin birnin Jenin, jigo ne a kungiyar da ke ikirarin jihadi a yankin Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye a yakin 1967.
A cewar kungiyar fursunonin Falasdinu, Isra’ila ta tsare Adnan har sau 12, inda ya shafe kusan shekaru takwas a kurkuku, akasari a karkashin tsarewar gwamnati.
Isra’ila ta zargi Adnan da goyon bayan ayyukan ta’addanci da alaka da kungiyar ’yan ta’adda da kuma tunzura jama’a.
Ya shiga yajin kin cin abinci akalla sau biyar a lokuta mabambanta da aka tsare shi tun shekara ta 2004.