Bafarawa na kokarin wargaza PDP a Jihar Sakkwato – Abdullahi MD
Wani jigo a Jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato Alhaji Abdullahi Yusuf MD ya zargi tsohon Gwamnan Jihar Attahiru Bafarawa da kokarin wargaza jam’iyyar a jihar musamman ma yadda aka gudanar da zaben shugabannin PDP na jihar a makonnin baya.Abdullahi MD ya ce, “Wannan abin kunya ne da ban takaici ganin yadda Alhaji Bafarawa ya yi […]
Wani jigo a Jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato Alhaji Abdullahi Yusuf MD ya zargi tsohon Gwamnan Jihar Attahiru Bafarawa da kokarin wargaza jam’iyyar a jihar musamman ma yadda aka gudanar da zaben shugabannin PDP na jihar a makonnin baya.
Abdullahi MD ya ce, “Wannan abin kunya ne da ban takaici ganin yadda Alhaji Bafarawa ya yi kaka-gida a zaben don dora wa mutane wanda ya ga dama.”
Alhaji Abdullahi ya yi wadanan kalamai ne ga manema labarai a makon jiya inda ya ce a sanina ba wani zaben shugabannin PDP da aka gudanar a jihar saboda dora wani mutum saman kujera, ba zabe ne ba don haka sun riga sun tafi kotu domin nema wa ’yan asalin jam’iyyar ta PDP adalci.
“Shugabanni da aka zaba sun karya dokar jam’iyya wanda kundinta ya nuna dole ne wadanda za su jagoranci mutane a jam’iyyar akalla su yi wata 20 cikin jam’iyya PDP wanda su ba su yi ba, kuma na tabbata kotu za ta yi mana adalci,” inji shi.
Alhaji Yusuf ya ce, “Bafarawa ya shigo PDP ne ya tarwatsa ta kawai kuma da alama akwai wata mummunar manufa da yake tare da ita kan jam’iyyarmu, in ka dubi halin mamaya da yake yi.”
Ya ce a lokacin da Bafarawa ya nuna bukatar shiga jam’iyyar sun yi farin ciki domin ba su yi tunani zai zo don tarwatsa tafiyarsu ba ga shi ya yi musu ba zata.
MD ya ce koda Bafarawa bai shiga PDP ba suna iya cin zabe domin ba ya cikin jam’iyyar suka ci Sanata daya da shugabannin kananan hukumomi 15 da ’yan majalisar wakilai da na jiha. Ya ce siyasar mamaya da Bafarawa ke yi ce ta hana shi samun kowace kujera a jihar tun lokacin da ya sauka daga mulki, kuma sun san wadanda suka sha wahala da shi a yanzu ba sa tare domin halinsa na mamaya.
A martanin wani na hannun daman Bafarawa Alhaji Abubakar Kantoma ya ce wadannan zarge-zarge ba su da tushe balle makama, zance ne na dan jagaliyar siyasa.
Alhaji Kantoma ya ce a lokacin zaben shugabannin jam’iyyar jami’an hukumar zabe da na tsaro da jagororin jam’iya a jihar duk sun halarta tare da Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Mukhtari Shagari da wakilan uwar jam’iyya ta kasa.
Ya ce Bafarawa uba ne a PDP, ya shigo ne don ya taimaka wa jama’ar Jihar Sakkwato a canja musu gwamnatin zalunci mai ci a yanzu, ba don ra’ayin kansa ko wani abu da zai samu ba.