Bafarawa ya ba da gudunmawar N1bn don cike giɓin da aka samu a mulkinsa
Bafarawa ya nemi gafarar jama’a kan duk wani laifi da ya aikata a lokacin da yake Gwamnan Sakkwato
A wannan Larabar ce tsohon Gwamnan Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayar da gudummawar Naira biliyan 1 a matsayin tallafi ga al’ummar jihar.
Ya bayyana cewa hakan ya samo asali ne daga burinsa na ganin ya cike duk wani giɓi da ya haifar a lokacin da yake kan riƙe akalar jagorancin jihar.
Bafarawa wanda ya mulki Jihar Sakkwato na tsawon wa’adi biyu a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, ya ce “a shekaru 70 na haihuwata, ina jin daɗin kyautatawa mutane.
“Burina a yanzu shi ne in tabbatar da cewa na cike duk wani giɓi da na haifar cikin rashin sani a sabanin haka wajen gudanar da dangantaka ta da jama’a a lokacin da nake kujerar mulki.
“Wasu na iya kiran wannan gudunmawa kaffara, amma na fi son a ɗauke ta a matsayin wani aiki na ramuwa. Ina so in mayar wa mutane kyakkyawar aniyya da ƙauna da suka nuna mini.
“Babu wani lokaci da wannan gudunmawar tawa za ta iya zama mai muhimmanci fiye da wannan lokaci da a yanzu jama’a ke cikin mawuyacin hali na ƙuncin rayuwa da ake fama da shi a ƙasar nan.
“A bisa wannan dalili ne na yanke shawarar samar da zunzurutun kuɗi har Naira biliyan 1 domin inganta jin daɗi da walwalar al’ummar Jihar Sakkwato,” in ji shi.
Sai dai ya nemi gafarar jama’a kan duk wani laifi da ya aikata a lokacin da yake gwamnan jihar.
Bafarawa ya bayyana cewa an damƙa wannan gudunmawar zuwa asusun wani kwamiti ƙarƙashin jagorancin Malam Lawal Maidoki, Shugaban Hukumar Zakka da Bayar da Tallafi ta Jihar Sakkwato.
Shi ma da yake jawabi a wajen taron, Sheikh Isa Talatan Mafara, ya shawarci kwamitin da ya yi la’akari da ‘yan gudun hijirar da suka fi buƙatar wannan tallafi.
Shugaban gidan Rediyon Vision FM, Shu’aibu Mungadi, ya yaba da halin kirki na tsohon gwamnan wanda ya bayyana a matsayin babban jagora.