Bafarawa ya nisanta kansa daga hotunansa da ake yadawa na takara

  Tsohon Gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa ya nisanta kansa daga takardun da ke nuna shi a matsayin dan takarar neman shugabancin kasa. Bafarawa ya ce yana neman tikitin neman jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takarar shugaban kasa a zaben shekara mai zuwa. A sanarwar da ya sanya wa hannu, Bafarawa ya ce […]

Bafarawa ya nisanta kansa daga hotunansa da ake yadawa na takara

 
Tsohon Gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa ya nisanta kansa daga takardun da ke nuna shi a matsayin dan takarar neman shugabancin kasa.
Bafarawa ya ce yana neman tikitin neman jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takarar shugaban kasa a zaben shekara mai zuwa.
A sanarwar da ya sanya wa hannu, Bafarawa ya ce lokaci bai yi ba da mutane za su fara fitar da hotunansu na neman takara.