Bafarawa ya yi daidai

Babu zato, kuma babu tsammani, kwatsam sai labarin da nake ta ji kamar daga sama, wai tsohon gwamnan jihar Sakkwato, kuma tsohon dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar DPP, Waton Alhaji Attahiru dalhatu Bafarawa ya canza sheka zuwa PDP ta tabbata gaskiya! Tabbas da mamaki, kuma na kara tabbatar da komai na iya faruwa akan […]

Bafarawa ya yi daidai

Babu zato, kuma babu tsammani, kwatsam sai labarin da nake ta ji kamar daga sama, wai tsohon gwamnan jihar Sakkwato, kuma tsohon dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar DPP, Waton Alhaji Attahiru dalhatu Bafarawa ya canza sheka zuwa PDP ta tabbata gaskiya! Tabbas da mamaki, kuma na kara tabbatar da komai na iya faruwa akan kowa ma, idan dai ba abu ne da Allah Ya tabbatar da cewa ba zai faru ba.
Yanzu dai duk ba shi ne abin magana akai ba! Bafarawa dai ya riga ya canza sheka. Shin canza shekarsa daidai ne ko kuma ya lamarin yake? To kafin aje ko ina dai, lallai na yarda cewa jam’iyyar PDP ba jam’iyyar kirki ba ce. Kuma ni ba na son jam’iyyar PDP, koda da munafunci, sannan kuma ba na nufinta da alkhairi. Amma dai Bafarawa ya yi daidai da ya koma PDP.
Na farko dai, shi Alun da ya bar PDP zuwa APC, ba don Allah ko domin maslahar al’umma ya bar ta, sai dai domin maslahar kansa. Za ka iya lura da haka ne, idan ka tuna lokacin da Alun Ya bar jam’iyyara ANPP zuwa jam’iyyar PDP da rana tsaka. Shin wancan lokacin, shi Alun bai san cewa PDP ba alkahairi ba ce ga al’umma? Amsar ita ce ya sani! Har ma ya fi ni da kai sanin hakan. Amma saboda a ido rufe yake neman shugabancin, sai ya bi PDP.
Na biyu, lokacin da mulkin PDP ya fara zama sanadiyar mutuwar daruruwan mutane, shin Alu bai san da cewa ya kamata ya bar jam’iyyar PDP ba har sai ranar da jam’iyyar ta fara dakatar da shi daga zama daya daga cikin manbobinta? Wannan kadai ya isa mu gane cewa Alu ba don Allah ko al’umma ya bar PDP zuwa APC ba.
Wannan tsokacin da na yi a sama, ishara ce kawai ga masu ganin cewa kamar Alu ya bar PDP don ya ceci al’umma, shi kuma Bafarawa ya shiga PDP don ba ya kishin al’umma.
Zancen abin da ya sa Bafarawa bai yi laifi da ya shiga PDP ba kuwa, za mu iya cewa wannan lamari bayyane yake. Ya za ayi Bafarawa ya zauna jam’iyya daya da Alu kuma Alu a matsayin jagora tsakaninku da Allah? Babu yadda za a yi zaman Alu da Bafarawa ya yi. Wannan kuma saboda bala’in tabarbarewar tarbiya da mulkin na Alu ya haifar a jihar.
Wannnan ba magana ce ta kishin al’umma ko kuma aikin ciyar da al’umma gaba ba, ko kusa. Zancen ya wuce nan. Zance ne ake yi akan yadda tarbiya ta yi karamci. Ba na zaton duk wani mutum da ya yi imani da Allah, koda ko kirista ne yayi gurin kasancewar ’ya’yansa a cikin lalaci da rashin sanin ya kamata. Koda ko za a mallaka masa duk arzikin wannan kasa ne a tafin hannunsa. Saboda haka, jama’a sun gaji da irin wannan mulki da ba ya koyar da tarbiya. Da wannan dalili, muke cewa duk jam’iyyar da wani mai karfin iya karo da Alu zai shiga domin ya kawar da shi, to muna maraba.
Abin lura kawai shi ne, ko Bafarawa ko ba Bafarawa ba, ko musulmi ko ba musulmi, duk wanda zai iya tabbatar da al’umma akan kyawawan dabi’u, shi ne ya kamata ya jagoranci al’umma. Kuma taimakon neman gyara ne, haka ma murkushe ma’abuci barna gyara ne.
Yanzu mu dauki Jihar Kano a matsayin misali, idan tsohon Gwamna Shekarau ya koma PDP akan kawai wannan takaddamar ta shugabancin jam’iyya, bai yi mutanen Kano da al’ummarsa adalci ba. Saboda me? Saboda Kwankwaso ya yi iya kokarinsa wajen tabbatar da tarbiya. Wannan kuma a fili yake, mai son karin bayani sai yaje yayi bincike akan ayukkan da hisba ta gabatar a jihar.
Shi kan shi fa Kwankwaso ni ba na ganin girmansa, saboda shi ma ya bar PDP ne saboda gudun takobin Tsohon can da ya yi ritaya bisa ga cilas, waton Bamanga Tukur. Amma kuma ina rokon Allah Ya yi masa albarka bisa kokarin tabbatar da tarbiya a jihar Kano. Za mu iya cewa, bakar tukunya ce ta fitar da farin tuwo. Illa dai kawai ita PDP , fitinar ta ta fi alkhairinta yawa da kashi tis’in bisa dari. Don haka muke kyamar ta kuma muke son mutanen kirki su nisance ta.
Abinda dai nake son in ce a nan shi ne, Bafarawa yana da uzurin komawa PDP domin ta kowane hali, akwai bukatar mulkin Sakkwato ya fita daga hannun masu yin sa a halin yanzu. Don haka ya yi daidai kuma ya burge ni, amma fa tare da haka, ni dai ba zan taba zaben PDP ba da yardar Allah. Amma ina rokon al’umma da su taimaka a kawar da gwamnati mai ci yanzu a jihar Sakkwato
Muhammad Arabi Umar, za a iya samunsa a kan wannan lambar 08024576898 (tedt kawai).

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno