Baffa Hotoro ya nemi afuwar Sheikh Dahiru Bauchi a hannun DSS

Baffa Hotoro ya ce, zai yi duk iya kokarinsa wajen ganin ya taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Baffa Hotoro ya nemi afuwar Sheikh Dahiru Bauchi a hannun DSS

Malamin nan da hukumar tsaro ta DSS ke tsare da shi kan zargin batanci ga Annabi Muhammadu (SAW) Adana Zubairu Adam (Baffa Hotoro) ya nemi afuwa fitaccen malamin Darikar Tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Baffa Hotoro ya nemi afuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi daga inda yake tsare a hannun DSS ne bayan iyalan shehun malamin sun yi korafi a kan irin zagin cin mutuncin da ya yi masa.

A ranar Juma’a Baffa Hotoro ya bayyana cewa “Ina neman afuwar Shaikh Dahiru Usman Bauchi da dukkanin iyalansa bisa kuskuren da na yi a baya. Haka kuma ba zan sake irin wannan a nan gaba ba.”

Da yake neman afuwar, Baffa Hotoro ya ce, zai yi duk iya kokarinsa wajen ganin ya taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Hukumar DSS ta tsare Baffa Hotoro wanda ya yi shuhura wajen sakin baki a karatuttukansa, ne bayan samun korafe-korafe masu yawa a kansa na neman tayar da zaune-tsaye.

Zarge-zargen sun sun hada da wanda Gwamnatin Jihar Kano take masa na yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Ukraine ta cimma yarjejeniya da Amurka kan haƙar ma’adinai

Dangote ya rage farashin man fetur zuwa N860 a Legas

Na gaji bashin 8.9bn a matsayin shugaban APC — Ganduje

Boko Haram sun sace mutum 2 da kayan abinci a Borno