Bafulani ba ya fada haka kawai – Sale Bayari

Alhaji Sale Bayari shi ne  sakataren sabuwar kungiyar nan ta  cigaban al’ummar fulani a Nijeriya [GAFDAN] kuma   tsohon sakataren kungiyar makiyaya ta  Miyetti Allah ta Nijeriya. A wannan tattaunawar ya kare al’ummar fulanin kan zarge-zargen da ake yi masu: Aminiya; Me za ka ce kan zarge-zargen da ake yi wa al’ummar Fulani kan  kai hare-hare   […]

Bafulani ba ya fada haka kawai – Sale Bayari

Alhaji Sale Bayari shi ne  sakataren sabuwar kungiyar nan ta  cigaban al’ummar fulani a Nijeriya [GAFDAN] kuma   tsohon sakataren kungiyar makiyaya ta  Miyetti Allah ta Nijeriya. A wannan tattaunawar ya kare al’ummar fulanin kan zarge-zargen da ake yi masu:

 Alhaji Sale Bayare

Aminiya; Me za ka ce kan zarge-zargen da ake yi wa al’ummar Fulani kan  kai hare-hare   a Nijeriya?
Sale Bayari: To, abubuwan da kowa ya sani ne a Nijeriya cewa  a cikin shekaru 16 da suka gabata  na mulkin farar hula an koma wata irin rayuwa ta siyasa, wadda wasu suka dauka idan ba su hargitsa al’amaru a addinance ko a kabilance ba, ba  za su ci zabe ba. Wannan shi ne ya jawo mana rikice-rikice  iri-iri a Nijeriya, musamman a yankin Arewa ta tsakiya da wasu suke kira Midle Belt. A wannan yanki na Arewa ta tsakiya aka dauko wani ra’ayi na kiyayya ga al’ummar hausawa da fulani  aka sanya su a gaba.  Ko a nan jihar Filato a lokacin da aka yi rikicin Jos na ranar 7 ga watan 9 na shekarar  2001, ta’adin da aka yi wa  al’ummarmu a irin yankunan   Barikin Ladi da Riyom da Jos ta Kudu suna da yawa. A lokacin da aka kira mu gaban kwamitin binciken wannan rikici na Mai shari’a Niki Tobi, mun kai lissafin mutanen da aka kashe mana a wannan rikici na mata da kananan yara. A lokacin ne aka gano cewa a kashi 70 bisa 100 na mutanen  da aka kashe a wannan rikici mutanenmu ne.
Ko a matsayin gwamnati da tsohon gwamnan jihar Filato Jonah Jang ya fitar kan wannan rikici, a shekarar 2009 ya nuna irin dimbin mutanen da aka kashe mana  a wadannan yankuna. A lokaci ‘yan kudu saboda suna da jaridu sai aka samu hadin kai na bangaren kabilanci da bangaren addini, kafin ka ce haka, sai masu neman kuri’a a Arewa  suka zo suka hade da wasu mutanen Arewa.  Sai ya zamanto  a lokacin tun da shugabannin kasar daga kudu suke,  sai suka rika amfani da irin wadannan rikice-rikice.  Kowa ya zamanto yana amfani da siyasar kabilanci da addini a lokacin don samun biyan bukata.
Duk inda ake zargin fulani da rikice-rikice idan ka duba za ka ga akwai kabilanci da addini a ciki. Kuma duk abin da ya faru idan kai  ba bafulatani ba ne  ko kuma kai bahaushe ne, ba za a ji komai ba. Amma idan kai wani yare ne, dan Arewa ko dan Kudu, idan wani abu ya same ka duk sai ka ji Nijeriya baki daya ta amsa.
A shekarar 2013 an kira mu a Majalisar  Wakilai  inda ake son ayi dokar samun burtali  da makiyaya ga fulani makiyaya a Nijeriya. Muka je muka gabatar da dalilan da suka sanya muke son a samar da burtaloli da wuraren kiwo ga fulani makiyaya a Nijeriya. Kafin kace kwabo sai aka mayar da wannan abu zuwa ga addini, haka ‘yan Arewa wadanda ba musulmi ba, da ‘yan Kudu wadanda ba musulmi ba, suka hade aka dakile wannan doka.
Idan ana son a zauna lafiya, kuma dukkanmu mun yarda cewa mu ‘yan Nijeriya ne, abin da ya samu wani daga cikinmu, ko na alheri ko na bakin ciki ya shafi kowa daga cikinmu. Duk inda kaji an taba bafulatani idan ba a mayar da hankali ba. Ko ba-jima ko ba-dade za ka ji wani abu ya faru a wajen. Saboda haka nake gaya wa jama’a cewa idan kun ji bafulatani ya taba wasu mutane a wani waje, to a tambayi mutanen nan su fadi gaskiya tsakaninsu da Allah, ba su yi wa fulanin nan wani abu ba? Domin gaskiyar magana, idan ka samu fulani sun je sun  taba wasu mutane a wani wuri to a binciki wadannan   mutanen su   fadi mene ne suka yi wa fulanin? Idan suka ce ba su yi masu komai   ba,  to wannan abin da aka yi masu ba fulani ba ne, wasu ne daban.

Aminiya; Wato a ganinka irin takurawar da ake yi wa fulani a kasar nan shi ne yake kawo wadannan rikice-rikice da suke faruwa?
Sale Bayari: kwarai kuwa, domin takurawar da ake yi wa fulani a Nijeriya ta kai inda ta kai. Domin akwai takurawar da fulani  suke fuskanta a Nijeriya ta irin  yanayin yau, akwai kuma takurawa ta muhalli da Allah Ya kawo. Wato kamar dumamar yanayi da Allah Ya kawo, domin a yau duk inda ake zaune a duniya za ka ga mutanen da suke zama a Arewa suna kaura suna suna komawa Kudu, saboda ruwa yana da ta barin Arewa yana komawa Kudu. Don haka a yau mutanen Nijar babu yadda za a yi su nufi Arewa su ce za su yi kiwo, sai dai su taho Kudu don kiwo. Haka mutane Chadi da Mali da Kamaru, duk idan suka tashi Kudu suke tahowa. Kuma babu yadda za a yi a Nijeriya a ce wani dan Nijeriya ba zai je wani wuri  ya zauna ba. A da fulanin da suke zaune a  Sakkwato da Zamfara da Katsina da Jigawa da dai sauransu, ruwan da ke wuraren ya ishe su rani da damina. Amma yanzu gabaki daya wadannan wurare sun bushe saboda canjin yanayi na muhalli. Saboda haka manoma yanzu ba sa samun amfanin gona kamar yadda suke samu a da.
Saboda haka babu yadda za a yi makiyayi ya zauna wurin da babu ruwa da ciyawa. Kuma a ce bafulatani bai isa ya je Kudu ba, duk da cewa duk Nijeriya ce. Alhalin su ma mutanen Kudu suna tashi suna zuwa ko’ina a Nijeriya suna gudanar da harkokinsu. Suna zuwa Maiduguri da Sakkwato da Adamawa da Kano suna harkokinsu.